Ran 11 ga wata a Brussels, Mr. Javier Solana wakili mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro na kungiyar EU ya yi shawarwari a asirce a kan shirin da kasashen shida suka gabatar tare da Mr. Ali Larijani sakataren kwamitin koli na tsaron kasa kuma wakilin farko na shawarwarin nukiliyar kasar Iran wanda ya kai ziyara a wurin, amma bangarorin biyu ba su bayyana abubuwan da suka tattauna ba.
A taron manema labaru da aka yi bayan shawarwarin, Solana ya ce, an yi wannan taron don shirya shawarwarin Paris da za a yi a ran 12 ga wata tsakanin kasashen shida a matsayin ministocin harkokin waje. Larijani ya ce, ana bukatar dogon lokaci wajen warware matsalar nukiliyar kasar Iran, ya kamata bangarorin dabam daban su yi hakuri.
A wannan rana kuma shugaba Mahmud Ahmadinejad ya sake jaddada cewa, kasar Iran ta tsai da kuduri don kiyaye ikonta wajen nukiliya, ba za ta daina ba.
|