Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-11 20:41:31    
Tsohon gari mai suna Pingyao na kasar Sin

cri

Tsohon gari da ake kira Pingyao cikin Sinanci yana tsakiyar lardin Shanxi da ke a arewacin kasar Sin, yana da nisan kilomita 90 daga kudancin birnin Taiyuan, fadar gwamnatin lardin Shanxi. Tsohon garin nan yana nan sumul garau har ba safai a kan ga irinsa ba a kasar Sin. Yau sama da shekaru 2700 ke nan da fara gina shi. Garin nan ya fi samun yalwa ne a zamanin daular Ming da ta Qing wato tsakanin shekarar 1368 zuwa ta 1911. Gine-gine da yawa da ke kasancewa a tsohon garin nan an yi su ne a cikin wadannan shekaru.

Idan an dubi tsohon garin Pingyao daga ganuwar garin, to, za a gano cewa, siffar garin ya tashi tamkar wani kunkuru. Gidajen jama'a da kantuna na garin siffarsu ta yi tamkar kokon bayan kunkuru, yayin da kofar kudu ta garin ta yi kamar kan kunkuru, haka nan kuma rijiyoyi biyu da ke waje da kofar sun yi kamar idanun kunkuru biyu, ban da wadannan kuma kofar arewa ta garin ta yi kamar wutsiyar kunkuru.

A cikin tsohon garin nan, akwai manyan hanyoyi guda 4 da matsakaitan hanyoyi 8 da kuma matsattsun hanyoyi da yawansu ya wuce 400. Sa'an nan kuma yawan gidaje masu tsakar gida da aka bari cikin dogon lokaci ya kai kimanin 4000, daga cikinsu akwai tsoffafin gidaje masu tsakar gida da yawansu ya wuce 400 suna nan sumul garau. Yanzu an mayar da irin wadannan tsoffafin gidaje da su zama otel-otel.

Wani hotel da ake kira "Tianyuankui" cikin Sinanci yana daya daga cikin irin wadannan otel-otel. Malam Wang Da, dan yawon shakatawa wanda ya shafe 'yan kwanaki yana kwana a wannan hotel ya bayyana cewa, "dakin kwana na hotel din nan bakon abu ne gare ni. Kayayyakin alatu na dakin irin na zamanin daular Ming da ta Qing ne. An manna takardun kalmomi da zane-zane irin na gargajiya a kan bangayen dakin. Ban da wadannan abubuwa kuma akwai telebijin mai launi da iya-kwandishan a dakin. Dakin yana da tsabta kwarai."

Wani hotel daban da ake kira "Yide" ma an gina shi ne daidai lokacin da aka gina hotel mai suna "Tianyuankui". A wancan lokaci, wannan hotel tsohon gidan wani ma'aikacin banki ne da ake kira Hou Wangbin. Hotel din nan ya kasu cikin gidaje 6, sa'an nan an mayar da su da su zama dakunan kwana, inda aka ajiye tsoffafin kayayyakin alatu masu kyau kwarai. Daga abubuwa masu kyau da aka sassaka a kan wadannan kayayyakin alatu da zane-zanensu, an iya gano cewa, wannan marigayi ma'aikacin banki mai hannu da shuni ne a wancan zamani. Malam Xu Linjie wanda ke yin aikin koyarwa a Jami'ar Beijing ya sha zuwa garin Pingyao, amma duk lokacin zuwansa a garin, sai ya kwana a wannan hotel mai suna "Yide". Ya bayyana cewa, "duk tsoffafin kayayyaki na wannan hotel suna nan sumul garau. Daga cikinsu, a farfajiyar wannan hotel, akwai wani babban dutse da ke bayan kofar hotel din da aka sassaka kalmomi da ke cewa "sannu da zuwa" da tsohon turken da aka yi da dutse, da dutse da a kan taka don hawan doki. Bayan da na koma hotel daga yawon shakatawa, na zagaya farfajiyar, sai na ji kamar ina ziyarar wani dakin nunin kayayyakin jama'a irin na gargajiya."

Ban da wadannan otel-otle biyu, kuma akwai wani hotel daban da ba safai a kan iya samunsa ba a sauran wurare. Sunan hotel din shi ne "Yamenguanshe" cikin Sinanci. A zamanin da, hotel din ya kan saukar da hakimai da sauran jami'an hukumomi. Yanzu idan wani bako ya kwana a wannan hotel kuma ya shiga cikin mashayarsa, to, zai iya amfani da littattafai da VCD da aka shirya yadda ya ga dama, ya karanta su ko kuma ya kallaci film din VCD kamar yadda a gidansa yake. Malama mai suna Luo Yaping wadda ke aiki a mashayar nan ta bayyana cewa, "a da mashayar nan dakin liyafa ne. Wadanda suka kwana a hotel din ko suka shirya liyafa dukansu manyan jami'ai ne. Ko da yake dakin ba ya da girma sosai, amma shi babban daki ne a wancan zamani." (Halilu)