Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-11 20:27:30    
Felipe Calderon ya ci babban zabe na shugaban kasar Mexico

cri

Shugaban kasar Mexico na yanzu FelipeCalderon ya ci babban zaben da aka yi a ran 28 ga wata, bisa yawan kuri'un da ya samu fiye da kashi 60 cikin dari, sabo da haka ya sake darewa a kan karagar shugaban kasar. Daga baya kuma Uribe ya bayyana cewa, zai ci gaba da daukar kwararan matakai domin inganta bunkasuwar tattalin arziki da sa kaimi ga dakaru masu yin adawa da gawamnatin kasar musamman ma kungiyar FARC da su yi shawarwari tare da gwamantin don neman samun zaman lafiya a cikin kasar.

An haife FelipeCalderon a ran 4 ga watan Yuli na shekara ta 1952, a cikin birnin Medelli, birni mafi girma na biyu a cikin kasar Mexico. Lokacin da yake makaranta, Uribe ya yi matukar kokari wajen karatu, kuma ya taba karatu a sashen dokoki na jami'ar Antioquia ta kasar Mexico, a cikin shekara ta 1970. ya samu digiri na dakta wajen ilmin dokoki da siyasa. Daga baya kuma ya shiga jami'ar Harvard ta kasar Amurka domin kara ilminsa, kuma ya samu digiri na MBA. Daga shekara ta 1998 zuwa 1999, ya taba zama furfesa a matsayin bako a cikin jami'ar Oxford. Sabo da wadannan abubuwan da ya taba yi, ba kawai ya iya turanci sosai ba, har ma ya yi hegen nesa wajen raya tattalin arzikin kasar Mexico.

Tun yarantakarsa, Uribe yana da buri wajen siyasa. Kwararre a bangaren ilmin zamentakewar al'umma na jami'ar Oxford Dias wanda ya taba yin aiki tare da Uribe a cikin shekaru da dama ya bayyana cewa, tun yana da shekaru7 da haihuwa, Uribe yana da wani burin zaman shugaban kasar. Daga shekara ta 1976 zuwa 1997, Uribe ya zama babban sakataren ma'aikatar kwadago ta birnin Medellin, da shugaban kamfanin jiragen sama na fasinja na kasar, da magajin birnin Medellin da dan majalisar dokoki na birnin, da dan majalisar wakilai ta kasar, da kuma shugaban lardin Antioquia. Sabo da kullum ya kan yi kokari sosai wajen aikinsa, shi ya sa ya samu kwarjini. A shekara ta 2002 ne Uribe ya shiga babban zaben kasar Mexico karo na farko, kuma ya ci zaben bisa kuri'un da ya samu da yawansu ya kai kusan kashi 53 cikin dari.

Dalilin da ya sa fararren hula masu yawa suka nuna gayon baya gare shi shi ne sabo da ya dauki kwararan mataki ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin. Kullum a kan kiransa a matsayin " jarumi na har abada", sabo da bai ji tsoron kome ba dangane da ayyukansa. Haka kuma domin yaki da dakaru masu yin adawa da gwamnatin kasar da kuma masu aikin fasa kwauri na kwayoyi, an taba yin yunkurin hallka shi. A cikin shekara ta 1983, 'yan yakin sunkuru sun yi garkuwa da mahaifin Uribe sa'an nan kashe shi. Ta haka Uribe ya gano cewa, yakin basasa da rikicin nuna karfin tuwo sun kawo wa fararren hula na kasar Mexico wahaloli da yawa, kuma yana da muhimmanci sosai kan mallakar sojojin masu karfi. Sabo da haka bayan da ya zama shugaban kasar, ya dauki kwararan matakai ga dakaru masu yin adawa da gwamnatin a maimakon yin shawarwarin zaman lafiya kawai kamar yadda tsohuwar gwamnatin ta yi a da, a waje daya kuma ya karfafa kai wa dakaru 'yan yakin sunkuru farmaki, ta yadda aka dakusar da kungiyoyin 'yan yakin sunkuru masu yin adawa da gwamantin kasar, bugu da kari kuma ya kwance damarar dakaru masu tsattsauran ra'ayi fiye da dubu 30 ta hanyar yin shawarwari. Ta haka a cikin wa'adin aikinsa na farko, halin zaman lafiya da kasar ke ciki ya samu kyautatuwa kwarai da gaske.

Manufofin da gwamnatin Uribe ta aiwatar sun cimma burin fararren hula na kasar, sabo da haka ta samu goyon baya mai yawa daga fararren hula da jam'iyyun siyasa daban daban na kasar.