Yau ran 11 ga wata, rana ce ta yawan jama'a ta duniya. Babban jigon wannan rana da kasar Sin ta tsai da a wannan shekara shi ne 'nuna kulawa ga yara mata'. Mr.Zhang Weiqing, shugaban kwamitin kula da yawan jama'a da kayyade iyali na kasar Sin, ya bayyana cewa, a shekarun nan, kasar Sin ta mai da muhimmanci sosai a kan batun rashin samun daidaici tsakanin yawan jarirai maza da kuma mata da aka haifa, kuma ta riga ta dauki matakai da dama, don neman daidaita irin wannan halin da ake ciki. Ban da wannan, ta kuma yi kokarin kago wani yanayi mai kyau ga yara mata.
Bisa kidayar mutane da gwamnatin kasar Sin ta yi a shekara ta 2000, an ce, a cikin ko wane rukunin jarirai, ana iya samun jarirai maza 119 a yayin da ake iya samun mata 100, wato an rasa samun daidaici a tsakanin jarirai maza da kuma jarirai mata ke nan. Wannan ya karya 'yancin mata da yara, haka kuma ya kawo tasiri mai tsanani a kan aikin kyautata tsarin yawan jama'ar kasar Sin. Mr.Zhang WeiQing ya ce, a halin yanzu, kasar Sin ta riga ta dauki matakai don neman daidaita irin wannan halin da ake ciki. 'A cikin 'yan shekarun nan, an yi ta samun babban bambanci tsakanin yawan jarirai maza da kuma mata a nan kasar Sin, wannan ya jawo hankulan gwamnati sosai. Tun daga shekara ta 2003, kwamitin kula da yawan jama'a da kayyade iyali na kasar Sin ya fara gwajin shirin nuna kulawa ga yara mata a wasu wurare, kuma sannu a hankali ne aka fara tsara wasu manufofin tattalin arziki da kuma kafa tsarin ba da tabbaci wadanda za su amfana wa yara mata da kuma iyalansu, don kiyaye moriyar mata da yara, kuma an yi kokarin neman hanyoyin da za a bi wajen daidaita matsalar samun babban bambancin yawan jarirai maza da mata.'
Mr.Zhang ya kara da cewa, ra'ayin nuna bambanci tsakanin maza da mata da wasu mutane ke da shi a wasu wuraren kasar Sin da tattalin arzikinsu ke baya baya shi ne babban dalilin da ya haifar da matsalar rashin samun daidaici tsakanin jarirai maza da mata. Musamman ma a cikin kauyuka, maza suna da muhimmanci, domin suna yin aikin karfi domin taimaka wa iyali. Idan aka haifi jaririya, to, da ta girma ta yi aure, iyayenta za su sha wahala sosai lokacin da suka tsufa. Irin wannan damuwa ta sa wasu mutane suke ta yin kokarin neman haifar yara maza, har ma ta haramtacciyar hanyar likitanci.
Shirin 'nuna kulawa ga yara mata' da kasar Sin ta fara aiwatarwa a wasu wurare a shekara ta 2003 shi ne ke neman daidaita hakikanan matsalolin da wasu iyalan da ke da mata suke fuskanta a fuskar aiki da zamantakewa, don ba su tallafi.
Mataimakiyar shugaban sashen ilmantarwa na kwamitin kula da yawan jama'a da kayyade iyali na birnin Beijing, Madam Liu Fengting ta ce, 'Da farko, za mu taimaka iyayensu a fannin tattalin arziki. Misali a wasu kauyuka, ana son bunkasa aikin samar da kayayyaki, amma ana fuskantar matsalar rashin kudi. To, a cikin irin wannan hali, za mu ba su rancen kudi kan dan karamin kudin ruwa kawai.. Na biyu kuwa, za mu bayar da kudin makaranta kai tsaya ga wannan yarinya, don taimaka musu shiga makaranta.'
Kasar Sin ta sami sakamako mai kyau a wajen aiwatar da 'shirin nuna kulawa ga yara mata' a shekaru uku da suka wuce, har ma ta sami goyon baya da amincewa daga wasu kungiyoyin duniya da ke nan kasar Sin. Wakilin asusun yara na MDD a nan kasar Sin, Mr.Christian Voumard ya ce, 'Ina fatan za a yi ta bunkasa wannan shiri, kuma mazauna karkara za su iya fahimta cewa, yara mata suna da muhimmanci daidai kamar maza. Nuna kulawa ga yara mata shi ne nuna kulawa ga makomar kasa.'
A halin yanzu dai, gwamnatin kasar Sin ta riga ta gabatar da cewa, ya zuwa shekara ta 2010, za a cimma daidaita bambancin yawan jarirai maza da mata kamar yadda ya kamata, kuma za a tabbatar da muhalli mai kyau ga ko wace yarinya kamar yadda ya kamata.(Lubabatu Lei)
|