
Ran 10 ga wata, kungiyar wasan kwallon kafa na kasashen duniya (FIFA) ta bayyana cewa, 'dan wasan kwallon kafa na kasar Faransa Zidane ya zama 'dan wasa mafi kyau na wasannin cin kofin duniya na shekarar 2006.

An riga an tabbatar da wannan sakamako kafin gasar karshe, Zidane ya zama na farko, shugaban kungiyar kasar Italiya Fabio Cannavarro ya zama na biyu, kuma 'dan wasa Andrea Pirlo ya zama na uku.
Zidane ya nuna cewa, bayan wasannin cin kofin duniya, zai bar aikinsa na 'dan wasan kwallon kafa.
|