Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-10 20:39:45    
Masana'antun sarrafa magunguna na kasar Sin sun kara karfinta wajen yin nazarin sabbin magunguna

cri

Kididdigar da aka yi ta nuna cewa, hukumar sa ido da kula da abinci da magunguna ta kasar Sin ta sami takardun neman lambar kirkira gomai kawai a ko wace shekara, ba a iya kwatanta su da yawan masana'antun sarrafa magunguna na kasar ba. Shugaban sashen magunguna na hukumar kula da kauyuka da bunkasuwar zaman al'umma ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin Mr. Yang Zhe ya bayyana cewa, yanzu magungunan da kasar Sin ta samar da su magunguna ne da ta kwaiwayi lambobin kirkira da kasashen waje suka taba yin rajista, amma wa'adinsu ya cika, yawansu ya kai fiye da kashi 97 cikin dari

'ma'anar kwaiwayar magunguna ita ce, wa'adin kiyaye lambar kirkira ya cika, mun iya samar da magani bisa lambar kirkirar, amma maganin da muka kera tsohon magani ne wanda bai iya shawo kan ciwace-ciwace yadda ya kamata ba. A galibi dai, bayan shekaru 10 da aka fara sayar da shi, mai yiwuwa ne za a fara kwaiwayi wannan magani.'

Donme da kyar masana'antun kasar Sin su yi nazari kan sabbin magunguna? An ba da karin haske cewa, da kyar sosai a yi nazari kan ko wane sabon magani, ba ma an yi amfani da kudi da yawa kawai ba, har ma an dade ana yin nazarin kan sabbin magunguna, a karshe dai, mai yiwuwa ne ba za a ci riba da yawa ba.

Don ingiza bunkaswar masana'antun sarrafa magunguna na kasar da kuma daga matsayin sana'ar sarrafa magunguna ta kasar, gwamnatin kasar Sin ta dauki matakan goyon baya da sa kaimi a jere a shekarun nan da suka wuce.

Da farko, gwamnatin kasar Sin ta kyautata manufofi, ta kayyade kwaiwayi magunguna daga wasu fannoni, ta haka ta ja gorar masana'antun sarrafa magunguna da su bi hanyar kirkiro. Na biyu kuma, ta kara zuba jari kan yin nazarin sabbin magunguna. Mataimakin shugaban hukumar kula da kauyuka da bunkasuwar zaman al'umma ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Mr. Sun Hongfu ya ce, 'a cikin shekaru 5 da suka gabata, ma'aikatarmu ta zuba kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan miliyan dari 9 kan yin nazarin sabbin magunguna kawai, amma mun iya sa kaimi kan wasu masana'antu da su zuba kudi a kan wannan. Sa'an nan kuma, kudin da muka zuba bai hada da wanda aka yi amfani da su domin ma'aikata ba, amma a kasashen waje kuma, an yi amfani da kudin da yawansa ya kai kahsi 40 cikin dari domin ma'aikata, ma iya cewa, mun zuba dukan kudade kan yin nazari. '

Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin tana nazarin ba masana'antu fifiko a fannin daukar haraji don sa kaimi kansu wajen yin nazarin sabbin magunguna.

Saboda kokarin da gwamnatin kasar Sin ke yi, masana'antun sarrafa magunguna masu yawa na kasar Sin sun kara dora muhimmanci kan yin nazarin sabbin magunguna.

Magungunan gargajiya na kasar Sin albarkatu ne na musamman da kasar Sin take da su a fannin yin nazarin sabbin magunguna. Ga misali, magani mai suna Artemisinin magani ne na farko da kasar Sin ta samar da shi da kanta bisa ilmin magungunan gargajiya na kasar Sin, wanda ke da amfani sosai wajen shawo kan ciwon zazzabin cizon sauro. Mr. Chen Qiyu, matamaikin shugaban kamfanin Fuxing na Shanghai da ke samar da wannan magani, ya bayyana cewa,'magungunan da aka saba yin amfani da su a Afirka ba su iya shawo kan ciwon zazzabin cizon sauro yadda ya kamata ba, ya zama banza ne, shi ya sa Kungiyar Kiwon Lafiya ta Duniya ta tsai da kudurin gabatar da maganin Artemisinin. A sakamakon haka, an kawo wa masana'antarmu makoma mai kyau, muna da kasuwa mai kyau.'

Yanzu masana'antun kasar Sin sun kara dora muhimmanci kan yin nazarin magungunan garajiya na kasar Sin a lokacin da suke nazarin sabbin magunguna, fifikon magungunan garajiya na kasar Sin ya kuma karfafa zukatan masana'antun kasar Sin wajen yin nazari kan sabbin magunguna.