Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-10 17:32:16    
Kasar Sin ta nemi da a mayar da wurarenta biyu, su zama tsoffin wuraren tarihi a duniya

cri

Ran 8 ga wata, a birnin Vilnius, hedkwatar kasar Lithuania, an yi taro na karo na 30 a kan tsoffafin wuraren tarihi a duniya, inda kasar Sin ta nemi da a mayar da wurarenta biyu wato wani wuri da dabbar Panda ke rayuwa da wani tsohon wurin tarihi mai suna "YIN", su zama tsoffafin wuraren tarihi a duniya.

Dabbar Panda wata irin dabba ce da ke dab da karewa a doron duniya, sabo da haka tana jawo hankulan mutanen duk duniya. A lardin Sichuan da ke a kudu maso yammacin kasar Sin, akwai wani wuri da dabbar nan ke rayuwa, wanda duka duka fadinsa ya kai kimanin muraba'in kilomita 10,000, musamman ma fadin wani karamin yanki da ke cikin wannan wuri da dabbar Panda ta fi zama ya kai muraba'in kilomita 5000. Wannan wuri yana da matukar muhimmanci ga kare ire-iren abubuwa masu rai. Haka zalika tsohon wurin tarihi mai suna "YIN" da ke a karkarar birnin Anyang na lardin Henan da ke a tsakiyar kasar Sin, ya taba zama hedkwatar kasar Sin a zamanin daula da ake kira "SHANG" cikin Sinanci wato yau sama da shekaru 3000 da suka wuce. Duk duk fadinsa ya kai kimanin muraba'in kilomita 24. Tun daga shekarar 1928 da aka fara tono tsoffin kayayyaki har zuwa yanzu, an riga an samu dimbin bayan kunkuru da aka sassaka kalmomi a jikinsu, da tsoffin kayayyakin tagulla da kuma sauran tsoffin kayayyakin tarihi wadanda ke da matukar muhimmanci ga yin binciken tsoffin al'adu na kasar Sin.

Da Malam Guo Zhan, wani jami'in ofishin kula da harkokin kayayyakin tarihi a duniya na hukumar kula da tsoffin kayayyaki ta kasar Sin ya tabo magana a kan batun neman mayar da wuraren kasar Sin da su zama tsoffin wuraren tarihi a duniya, sai ya ce, "kasar Sin wata makekiyar kasa ce. Matsayinta na tattalin arziki da al'adunta ya sha bamban a wurare daban daban. A wasu wurarenta ana mai da hankali sosai ga neman mayar da su da su zama tsoffin wuraren tarihi a duniya, amma ba su yi kokari sosai wajen kare su ba."

Malam Luo Zhewen wanda shekarunsa ya kai 82 da haihuwa a bana wani shahararren masanin ilmin kare tsoffin wurare na kasar Sin ne. Ya nuna cewa, kara kokarin kula da tsoffafin wuraren tarihi yana da muhimmanci a kasar Sin. Ya ce, "tun bayan da kasar Sin ta rattaba hannu a kan "yarjejeniyar kare tsoffin wuraren tarihi a duniya" a shekarar 1985, ba ma kawai kasarmu ta kan shiga harkoki da yarjejeniyar ta shafa ba, har ma tana kokarin neman mayar da wurarenta da su zama tsoffafin wuraren tarihi a duniya. Yanzu kasar Sin kasa ce mai tasowa a fannin yawan tsoffafin wurare a duniya. Amma abin da ya fi muhimmanci shi ne mu kara kokari sosai wajen kare wadannan tsoffafin wuraren tarihi a kasarmu. "

Dangane da taro kan tsoffin wuraren tarihi a duniya da aka yi a shekarar nan, kafofin watsa labaru na kasar Sin suna ganin cewa, mai yiwuwa ne, za a amince da mayar da wuraren biyu na kasar Sin wato wani wuri da dabbar Panda ke rayuwa da wani tsohon wurin tarihi mai suna "YIN", su zama tsoffafin wuraren tarihi a duniya. Amma Malam Guo Zhan, wani jami'in hukumar kula da tsoffin kayayyaki ta kasar Sin yana ganin cewa, "manufar da muke bi ba don neman yawan wuraren kasarmu da su zama tsoffafin wuraren tarihi a duniya ba, bamban da haka ya kamata, mu yi kokari wajen daga matsayinmu na kula da tsofaffin wuraren tarihi da ya kai daidai da na duniya. Mu kara gudanar da ayyukanmu na kare tsoffafin wuraren tarihi a duniya da kyau a fannoni daban daban. " ( Halilu )