Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-10 11:09:47    
Ana wasan kwaikwayo a kananan dakunan wasan kwaikwayo sosai cikin hali mai kokari a kasar Sin

cri

Tun daga farkon shekarar da muke ciki, kungiyoyin wasan kwaikwayo wadanda suka zo daga kasashe daban-daban su kan yi nune-nunen wasannin kwaikwayo da yawa a cikin kananan dakunan wasan kwaikwayo na garuruwa da biranen kasar Sin daban-daban. Masu sha'awar da wasannin kwaikwayo na kasar Sin suna farin ciki sosai domin kallon wadannan wasannin kwaikwayo da suke da halayen musamman iri iri.

A watan Nuwamba na shekarar 1982, an nuna wani karamin wasan kwaikwayo mai suna "Alamar da ake nune-nune a cikin wani jirgin kasa". Ba a shakkar da cewa, wannan karamin wasan kwaikwayo ne da aka yi nune-nune a nan kasar Sin ba. Wannan wasan kwaikwayo ya bayyana wata tatsuniyar da ta auku a cikin wani karshen dakin jirgin kasa. A cikin wani dare mai duhu sosai, wani ma'aikacin jirgin kasa da wani fasinja da wani dan fashi suna da tunaninsu daban-daban. A cikin kwakwarmayar da aka yi a tsakanin nauyin da aka dora musu da moriya radin kansu, an nuna halaye iri iri na wadannan mutane sosai. Sakamakon haka, wannan wasan kwaikwayo ya samu nasara sosai. A cikin tsawon kusan rabin shekara 1 kawai, an nuna wannan wasan kwaikwayo har sau fiye da dari 1. Tun wancan lokaci ne, an fara gina kananan dakunan wasan kwaikwayo a duk fadin kasar Sin, an kuma yi nune-nunen kananan wasannin kwaikwayo masu dimbin yawa a kai a kai.

Lokacin da ake nune-nuen kananan wasannin kwaikwayo, masu wasan kwaikwayo da masu kallon wasan kwaikwayo suna kusa sosai. Abubuwan da suke bulla a cikin zuciyoyin masu wasan kwaikwayo suna jawo hankulan masu kallo wasan kwaikwayo kwarai. Mr. Meng Jinghui, wani sannanen direkta ne da ya kan gwada sabbin salon wasannin kwaikwayo a nan kasar Sin. Mr. Meng ya ce, "A ganina, ko shakka babu a hada halayen wasannin kwaikwayo na zamani da na gargaji. Amma na fi son kago sabon salon wasannin kwaikwayo na zamani da suke bayyana halin zaman al'umma da muke ciki. Domin irin wadannan abubuwa namu ne, kuma za mu iya jin dadin kallonsu. Na kan fada wa kaina cewa, dole ne na tafi gaba da kwar jini domin wannan duniya a sabuwa take a kowace rana."

Halin musamman na kananan wasannin kwaikwayo na zamani na kasar Sin shi ne a kan mai da hankali sosai kan halin zaman rayuwar jama'a da ake ciki yanzu. Musamman a cikin kananan wasannin kwaikwayo da aka yi a cikin 'yan shekarun da suka wuce, a kan fi nuna irin wannan halin da ake ciki yanzu a nan kasar Sin.

Lokacin da yake ba da sharhi kan wannan halin musamman da kananan wasannin kwaikwayo suke bayyanawa a cikin 'yan shekarun da suka wuce, Mr. Gao Yi, wani malami ne da ke aiki a jami'ar koyon ilmin wasan kwaikwayo ta kasar Sin ya ce, "A farkon shekarun 90 na karnin da ya gabata, a kan bayyana wasu batutuwan zaman al'umma da ke jawo hankulan jama'a sosai a cikin kananan wasannin kwaikwayo, amma yanzu, an fara tattaunawa kan batutuwan da ke shafar tunanin dan Adam da yake kasancewa a cikin wani lokacin musamman. Alal misali, a kan bayyana batun rashin aikin yi da batun zuciyoyin dan Adam kuma da batun bambancin da ke kasancewa a tsakanin masu arziki da masu fama da talauci. Wadannan kananan wasannin kwaikwayo sun bayyana cewa, wasannin kwaikwayo suna mai da hankali kan zaman rayuwar jama'a sosai. A sa'i daya kuma, suna maido da tunanin girmama wa halaye iri iri na mutane."

Ba ma kawai ana nune-nunen sannanun wasannin kwaikwayo na kasar Sin a cikin dakunan kananan wasannin kwaikwayo ba, har ma ana nune-nunen jerin sannanun wasannin kwaikwayo na kasashen waje ciki har da "Wasan kwaikwayo na Kwabo Talatin" na Bertolt Brecht da "Babban mai rangadin aiki a madadin sarki" na Nikolas Vasilievich Gogol da "Gidan Dodo" na Henrik Ibsen da makamatansu. A shekara ta 2005, nune-nunen kananan wasannin kwaikwayo a nan kasar Sin ya kai wani sabon mataki sakamakon kafuwar karamin dakin wasan kwaikwayo mai suna "Oriental Pioneer" a cikin Gidan Wasan Kwaikwayo na kasar Sin. Mr. Fu Weibo, shugaban Gidan wasan kwaikwayo na kasar Sin ya ce, shi da takwarorinsa suna kokari kan yadda za a raya wannan dakin nune-nunen kananan wasannin kwaikwayo da ya zama wani wurin da za a yi musayar wasannin kwaikwayo na kasar Sin da na kasashen waje. Yanzu, wasannin kwaikwayo da ake nuna a cikin kananan dakunan wasan kwaikwayo yana ta zama muhimmin abu ga kasuwar al'adu ta kasar Sin. (Sanusi Chen)