|
 |
 |
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
 |
|
 |
|
|
 |
(GMT+08:00)
2006-07-10 11:03:44
|
Kungiyar Italy Ta zama zakara a Wasan kwallon kafa na Duniya a shekarar 2006 a Kasar Jamus
cri
 Wakilin Rediyon kasar Sin ya ruwaito mana labari cewa , a ran 10 ga watan Yuli da sassafe , agogon Beijing an rufe Wasan kwallon kafa na Duniya a shekarar 2006 a kasar Jamus wanda aka yi cikin wata daya . A cikin gasar ta karshe a cikin minti 120 kungiyar Italy da Kungiyar Faransa sun yi kunnen doki da kwallo daya da daya. A karshe dai ta hanyar bugu daga kai sai mai tsaron gida , Kungiyar Italy ta ci nasara kan Kungiyar Faransa da kwallo 6 da 4 . Wannan ne karo na 4 da Kungiyar Italy ta zama zakara a duniya a cikin tarihi .
An bude wannan wasan ne a ran 9 ga watan Yuni , an yi gasanni a cikin birane 12 na kasar Jamus . Kungiyoyin wasan kwallon kafa guda 32 na Kungiyar FIFA suka taka rawan gasanni guda 64 don samun lambawan .
Wasan kwallon kafa na duniya mai zuwa za a yi shi ne a kasar Afrika ta kudu a shekara 2010 . ( Ado)
|
|
|