Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-06 21:13:44    
Bunkasuwar kolejojin Confucius masu koyar da harshen Sinanci a ketare

cri

An gudanar da babban taro na kolejojin Confucius, wanda aka shafe kwanaki biyu ana yinsa a nan Beijing. An labarta, cewa wadannan kolejoji, wadanda muhimmin aikinsu shi ne koyar da harshen Sinanci suna nan suna samun bunkasuwa a kasashe da dama na ketare. A sa'I daya kuma, gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin nuna goyon baya ga ayyukan kolejojin Confucius gwargwadon iyawa, ta yadda za a samar da sauki ga dimbin mutane dake ketare wajen koyon harshen Sinanci.

Kolejin Confucius na Korea ta Kudu, an bude shi ne a shekarar 2004 a hukunce, wanda kuma koleji na farko ne da kasar Sin ta kafa a duk duniya. Yanzu akwai mutane 400 da suke koyon harshen Sinanci a nan. Malam Kim Ki Cheol yana daya daga cikinsu. Ya gaya wa wakilinmu, cewa: " Shekaru biyu ke nan da nake koyon Sinanci. Yanzu ina mai matukar sha'awar al'adun kasar Sin bayan na soma koyon Sinanci. Kasar Sin tana da girma, wadda kuma za ta iya samar mini da kyakkyawar dama ko a fannin neman aikin yi a kasar Sin ko a fannin yin cinikayya.

Madam Chen Zhili, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta yi jawabi a gun babban taron, inda ta fadi, cewa yanzu akwai kolejojin Confucius da kuma azuzuwan Confucius da yawansu ya zarce 80 suna koyar da harshen Sinanci a kasashe da jihohi 36. Kafuwar kolejojin Confucius tana da amfani ga kara cimma burin mutanen ketare dake kishin koyon harshen Sinanci, da kuma kara yin hadin gwiwa da musanye-musanye tsakanin kasar Sin da kasashe daban daban a fannin tattalin arziki da al'adu.

Aminai masu sauraro, ko kun san cewa, harshen Sinanci wani harshe ne mai sarkakiya musamman ma ga mutanen kasashen Yamma wadanda da kyar da sudin goshi suke koyon lafazin Sinanci da rubutunsa.

Amma, da yake kasar Sin ta kara yin gyare-gyare da bude kofa ga kasashen waje da samun bunkasuwar tattalin arziki da saurin gaske da kuma yin musanye-musanye tare da kasashe daban daban na duniya a ' yan shekarun baya, shi ya sa kamfanoni da masana'antu masu yawan gaske na ketare suka zuba jari a kasar Sin domin kafa ma'aikatu; Ban da wannan kuma baki da sukan zo nan kasar Sin domin yin aiki da yawon shakatawa sai kara karuwa suke a kowace rana. Kazalika, Sinawa da suka fita zuwa ketare domin yin dalibta ,da cinikayya da kuma yawon shakatawa su ma sun karu karuwar gaske. Saboda haka, mutane da yawa na kasashen waje sun shiga cikin jerin wadanda suke koyon Sinanci, wanda kuma suka mayar da shi a matsayin wani muhimmin kaya da suke yin amfani da shi wajen samun ilmi game da kasar Sin.

Bisa wannan hali dai, gwamnatin kasar Sin ta tsaida kudurin kafa kolejojin Confucius a ketare, wadanda suka zama tamkar sansanonin koyar da Sinanci ga mutane mazauna wuraren.

Mun samu labarin, cewa an kafa wadannan kolejojin Confufius ne daidai bisa bambancin halayen musamman na kasashe daban daban wajen koyar da Sinanci. Alal misali: A kolejin Confufius na Nairobi a kasar Kenya, akan koyar da harshen Sinanci ne ta hanyar bude darussan al'adu na kasar Sin. Yanzu, daliban wannan koleji ba ma kawai suna iya yin magana da harshen Sinanci ba gargada ba, har ma suna iya rera waka da wannan harshe.

Yayin da kolejojin Confufius suke samun bunkasuwa a kasashen waje, gwamnatin kasar Sin ta kuma dauki nauyin ci gaba da goyon bayan ayyukan kolejojin Confufius gwargwadon iyawa. Madam Chen Zhili ta furta, cewa : 'Gwamnatin kasar Sin tana so ta ba da sauki ga jama'ar kasashe daban daban wajen koyon Sinanci da kuma samun ilmi game da kasar Sin. Nan gaba, za mu yi muhimman ayyuka guda uku. Aiki na farko, shi ne za mu yi hadin gwiwa wajen yin aikin koyarwa bisa ka'idojin da suka shafi kolejojin Confufius ; Aiki na biyu, shi ne girmama dokokin shari'a na kasashen da aka kafa kolejoji a can da kuma nuna biyayya ga abubuwan al'ada na wurin ; Aiki na uku wato na karshe, shi ne takaita fasahohin da aka samu ba tare da bata lokaci ba da kuma kyautata tsarin kimanta ingancin aikin koyarwa.

Mun samu labarin, cewa ban da kolejojin Confufius da aka rigaya aka kafa, kuma akwai hukumomo fiye da 70 na kasashe sama da 30 da suka gabatar wa kasar Sin takardun rokon kafa irin wadannan kolejoji. (Sani Wang)