Ran 5 ga wata, Mr. Javier Solana wakili mai kula da harkokin waje da manufofin tsaro na kungiyar EU ya ce, zai yi shawarwari tare da Mr. Ali larijani wakilin farko na shawarwarin nukiliya na kasar Iran a ran 6 ga wata a Brussels.
A cikin wata sanarwa Mr. Javier Solana ya ce, lokacin da Larijani ya daga ziyararsa a Brussels, yana "jin ban mamaki sosai". Salona ya jaddada cewa, kungiyar EU tana son ta yi shawarwari tare da bangaren kasar Iran kan shirin da kasashen Amurka, Rasha?Sin, Birtaniya, Faransa da Jamus suka gabata don warware matsalar nukiliyar kasar Iran.
|