Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 20:30:07    
Mr Tian Changjie da dakinsa na yin nune-nunen al'adar gargajiyar kabilar Tujia

cri

Mr Tian Changjie mai shekaru 50 da haihuwa shi ne wani manomi dan kabilar Tujia na lardin Hubei na kasar Sin. Tun daga farkon shekaru 80 na karni na 20, ya yi amfani da kudinsa na kansa don tattara kayayyakin tarihi da suke da nasaba da kabilarsa, wato kabilar Tujia, kuma shi kansa ya kafa dakinsa na yin nune-nunen kayayyakin al'adar gargajiyar kabilar Tujia kafin wasu shekaru da suka wuce.

Mr Tian Changjie shi ne mutumin da ke zama a wani kauyen lardin Hubei. Ya taba aikin noma da nuna fasahar yin giya da dan kwadago mai aikin gyara hanya da mai daukar hoto da dai sauransu. Shi dan gajere ne , amma yana da hazikanci sosai, ya kasance cikin kokarin binciken abubuwa. A shekaru 80 na karni na 20, kasar Sin ta yi aikin kiyastar yawan mutanenta karo na uku , bayan binciken da aka yi, an tabbatar da cewa, Mr Tian Changjie da 'yan kauyensu su ne 'yan kabilar Tujia, amma a da, an yi musu rajistar kabilar Han. Wannan ya jawo sha'awar Mr Tian Changjie, ya bayyana cewa, kafin shekarar 1983, ba mu san cewa, mu ne 'yan kabilar Tujia. Tun daga ranar da aka haife mu, an gaya mana cewa, mu ne 'yan kabilar Han ne, don kara fahimtar tarihinmu da tabbatar da kabilar da muke ciki, sai na soma aikin tattara kayayyakin tarihi .

A cikin wasu 'yan shekarun da suka wuce, hanyar neman kudin kashewa da Mr Tian Changjie ya bi ita ce daukar hotuna. Ya kan je yawon daukar hotuna daga wannan kauye zuwa wancan kauye, amma a lokacin da ya dauki hotuna domin wasu mutane, sai ya tattara wasu kayayyakin tarihi na kabilarsa wato na kabilar Tujia ko saye su da labarai dangane da kabilar. A wannan lokaci, ya taba samun mutum mutumi guda biyu na duwatsu a cikin kungurmin daji. An ce, wadannan mutum mutumi guda biyu su ne kakanin kabilar Tujia, wato sarkin Xiang da sarauniyar da ake cewa" ruwan gishiri".

Mr Tian Changjie ya yi ta tattara kayayyakin tarihi ba tare da tsayawa ba, wani lokaci ma ya sayi kayayyakin tarihi ta hanyar daukar hotuna ko ya kashe kudade da yawa don sayen kayayyakin tarihi masu daraja sosai, a kai a kai ya tattara kayayyakin tarihi da suke kunshe da kayayyakin ado da tufaffi da tsofaffin littattafai da kayayyakin da ake yin amfani da su yau da kullum har da kayayyakin aiki da makamai da dai sauransu. A watan Augusta na shekarar 1993, Mr Tian Changjie ya shirya wani nuni a gidan nune-nune na gundumarsa, yawan kayayyakin tarihi ya kai 600 ko fiye, bayan nunin nan ya ba da kyautar wadannan kayayyaki ga gidan nune-nune na wannan gunduma. Mr Tian Changjie ya bayyana cewa, na tattara wadannan kayayyaki domin tabbatar da tarihi na kaina, amma ba domin sayar da su don samun kudi ba, bai kamata na sayar da su ba, duk domin tabbatar da cewa, mu ne 'yan kabilar Tujia.

Sa'anan kuma, Mr Tian Changjie ya sake tattara kayayyakin tarihi da yawansu ya kai dubu ko fiye, kuma ya rubuta bayanan musamman dangane da wadannan kayayyakin tarihi da ya tattara.

A ran 17 ga wannan wata, rana ce da Mr Tian Changjie ya yi farin ciki sosai, bisa taimakon kudin da gwamnatin wurin ta samar masa , ya sami damar bude dakinsa na nuna kayayyakin tarihi na gargajiyar kabilar Tujia, kodayake dakin nan ba ya da kyau sosai , amma kowane kayan da ya nuna na da daraja sosai.

A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, mutane da yawansu ya kai dubu goma sun kai ziyara a dakinsa na nune-nune, daga cikinsa da akwai kwararru da yawa wajen al'adar kabilu da suka zo daga wurare masu nesa, Mr Tian Changjie ya bayyana cewa, yana tsammanin cewa, zai kaura da dakin nan zuwa gunduma, domin nuna kayayyakin nan ga mutanen da suke zama a birane .(Halima)