Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 18:28:15    
Kasar Sin ta dauki matakai wajen hana yaduwar cututtukan ciwon Aids a tsakanin uwa da jariri

cri

Yaduwar ciwon Aids a tsakanin mai juna biyu da jariri yana daya cikin hanyoyi 3 na yada ciwon Aids a tsakanin mutane. Idan ba a dauki matakan da suka wajaba ba, mai ciki wadda ta kamu da ciwon Aids za ta yada cutar Aids ga jaririnta. Amma idan an yi mata jiyya, za a iya hana yaduwar ciwon Aids a tsakanin uwa da jariri. Sabo da haka, yanzu, gwamnatin kasar Sin tana daukan matakan da suka wajaba a gundummomi kusan dari 3 domin yin rigakafin yada ciwon Aids a tsakanin uwa da jariri. Wato, gwamnatin kasar Sin ta yi wa masu juna biyu jiyya ko ta dauki sauran matakan likitanci da suka wajaba, amma ba tare da karbar kudi ba. Ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta shelanta cewa, za a kara yin wannan aiki a yankuna daban-daban. Bisa shirin da aka tsara, ya zuwa shekara ta 2010, za a yi wannan aiki a gundummomin da suka kai kashi casa'in cikin kashi dari bisa na dukkan gundummomin kasar Sin.

Madam Hu, wata monamiya ce da ke da zama a lardin Yunnan. Yau da shekaru 3 da suka wuce, ta yi murna sosai domin ta samu ciki. Amma lokacin da ake duba lafiyarta, an gaya mata cewa ko da yake ta riga ta daina shan miyagun kwayoyi, amma ta riga ta kamu da cutar Aids. Idan da ba ta sha magani ba, jaririnta ma zai kamu da cutar Aids. Likitoci sun gaya mata cewa, idan tana so, gwamnati za ta yi mata jiyya, amma ba za ta biya kudi ba, domin hana yaduwar ciwon Aids a tsakaninta da jaririnta. Madam Hu ta zabi hanyar shan magani. Yanzu, jaririnta ya kai shekaru 2 da haihuwa, amma bai kamu da ciwon Aids ba.

Shehun malama Su Suiqing, wadda ke aiki a cibiyar yin rigakafi da shawo kan ciwace-ciwace ta kasar Sin ta ce, aikin hana yaduwar cutar Aids yana da muhimmanci sosai. "Bisa kwarya-kwaryar kididdigar da kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa ta yi, jarirai kimanin dubu dari 8 suna kamuwa da ciwon Aids a kowace shekara a duk fadin duniya. A nan kasar Sin, masana na kungiyar kiwon lafiya ta kasa da kasa sun kimanta cewa, yanzu jarirai dubu 9 ne suka kamu da ciwon Aids daga iyayensu mata wadanda suka kamu da ciwon Aids."

Shehun malama Su ta ce, muhimman matakan da aka dauka domin hana yaduwar ciwon Aids a tsakanin masu juna biyu da jarirai su ne, da farko dai, hukumomin kiwon lafiya na wurin sun ba da shawara ga masu juna biyu. Sannan kuma, idan masu juna biyu suna so, sai an bincike lafiyarsu domin tabbatar da cewa ko sun kamu da ciwon Aids. Daga baya, idan mai juna biyu ta kamu da ciwon Aids, amma ba ta son barin jaririnta, shi ke nan, gwamnati za ta samar mata magungunan ciwon Aids amma ba tare da karbar kudi daga mai juna biyu ba. Lokacin da mai juna biyu ta haihu, likitoci za su dauki matakai domin hana yaduwar cutar Aids ga jariri. Bayan haihuwar jariri, gwamnatin kasar Sin ta samar da garin madara ga jariri, kuma ta kan duba lafiyar jariri, amma ba ta samu kudi ba daga iyayen jariri ba.

A ran 5 ga wata, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta shirya taro a birnin Kunming na lardin Yunnan, inda hukumomin gwamnati da masana suka yi musayar ra'ayoyi da fasahohin da aka samu kan wannan aiki.

Mr. Yang Qing, direktan hukumar kula da lafiyar mata da jarirai a ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ya gaya wa wadanda suka halarci taron cewa, a shekarar bara, gwamnatin tsakiya ta kasar Sin ta zuba kudaden Renminbi yuan fiye da miliyan 40 kan aikin hana yaduwar cutar Aids a tsakanin mai juna biyu da jariri. Mr. Yang ya ce, "Bisa shirin aikin yin rigakafi da shawo kan ciwon Aids na kasar Sin da aka tsara, ya zuwa karshen shekara ta 2010, za a yi aikin hana yaduwar ciwon Aids a tsakanin masu juna biyu da jarirai a gundummomin da za su kai fiye da kashi casa'in cikin kashi dari na dukkan gundummomin kasar Sin. Ana fuskantar babban nauyin da ake dorawa domin cimma wannan buri."

Yanzu, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta riga ta nemi gwamnatocin wurare na kasar Sin da su kara yin wannan aiki bisa halin da suke ciki. Bugu da kari kuma, ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Sin ta riga ta ba da shawarce-shwarcen da za su iya ba da jagoranci kan yadda za a yi aikin hana yaduwar cutarn Aids a tsakanin masu juna biyu da jarirai. (Sanusi Chen)