Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 16:43:37    
Wakilin shawarwarin nukiliya na kasar Iran na farko ya bayyana cewa, kasar Iran za ta ba da amsa kan sabon shirin da kasashe 6 suka yi wajen ran 6 ga watan Agusta

cri
Ran 4 ga wata a Tehran, Ali Larijani, wakili a gun shawarwarin nukiliya na farko na kasar Iran, kuma sakataren babban kwamitin tsaron kasar ya bayyana cewa, watakila kasar Iran za ta ba da amsa kan sabon shirin da kasashe 6 suka yi wajen ran 6 ga watan Agusta. Amma, ya sake nanata cewa, kasar Iran ba za ta dakatar da ayyukan ta ce uranium mai inganci ba bisa bukatun da kasashen yamma suke.

Amma, a wannan rana Manouchehr Mottaki, ministan harkokin waje na kasar Iran ya bayyana cewa, kafin wannan, kasar Iran ta sanar da cewa, za ta ba da amsa a ran 22 ga watan Agusta, kuma ba za ta canja wannan lokaci ba.

Bisa labarin da muka samu an ce, Mr. Larijani, da Javier Solana, babban wakilin kungiyar tarayyar kasashen Turai mai kula da manufar harkokin waje da tsaron kasa za su yi shawarwari a ran 5 ga wata, bangarorin biyu za su yi tattaunawa kan wasu abubuwan da ke cikin sabon shiri na kasashe 6. (Bilkisu)