Bisa karshen kididdigar da ofishin kula da harkokin babban zabe na kasar Peru ya yi a ran 13 ga wata, an ce, 'dan takarar jam'iyyar Partido Aprista Peruano Alan Garcia ya sami nasara a gun babban zaben shugaban kasar Peru da samun kuri'a kashi 52.6 daga cikin dari. A ran 28 ga wata zai yi rantsuwar zaman shugaban kasar Peru.
An haifi Alan Garcia a ranar 23 ga watan Mayu na shekarar 1949. Ya taba karatu a jami'ar San Marcos. Bayan haka, ya je kasashen Spain da Faransa da Ingila da Holland domin kara samun ilmi, ya samu takardun digiri na shehun malami a fannonin shari'a da zaman al'umma. A shekarar 1976, ya koma kasar Peru, sa'an nan ya shiga cikin jam'iyyar Partido Aprista Peruano, wato ya fara zaman rayuwarsa na siyasa.
A shekarar 1982, Alan Garcia ya zama babban sakataren jam'iyyarsa. A shekarar 1985, ya sami nasarar babban zaben shugaban kasar Peru, sabo da haka Alan Garcia mai shekaru 36 da haihuwa ya zama shugaban kasar Peru.
A cikin shekaru 5 na shekaru 80 na karni da ya gabata a lokacin da yake shugaban kasar Peru, Alan Garcia ya gudanar da manufofin sa kaimi ga jam'arsa da su kara kashe kudi a kan kayayyakin masarufi, ta haka an kara samar da kayayyaki, haka kuma ya kayyade cewa, yawan kudin da kasar Peru ya biya basusukan duniya ya yi kasa da kashi 10 daga cikin dari na dukkan kudadden da kasar ta samu wajen cinikayyar waje. Sabo da haka, tattalin arzikin kasar ya kara samun bunkasuwa sosai, a shekarar 1986 da ta 1987, yawan karuwar tattalin arzikin kasar Peru ya kai kashi 8.9 da 6.7 daga cikin dari. Amma daga karshen rabin shekarar 1986, tattalin arzikin kasar Peru yana cikin mugun hali, ba ta da kudin musanya da yawa, farashin kayayyaki ya haura da gaske, hauhawar farashi ta tsananta sosai, wadda ta taba kai kashi dubu 7 da dari 6 daga cikin dari, matsayin zaman rayuwar jama'a ya ragu sosai.
Tare da raguwar tattalin arzikin kasar Peru, sha'anin siyasa na Alan Garcia ya taba bare. A watan Yuni na shekarar 1986, wasu fursunoni 'yan yakin sari-ka-noke na kungiyar Sendero Luminoso a giadjen kurkuku uku sun kama wasu mutane domin garkuwa da su, haka kuma sun bukaci gwamnatin kasar Peru ta amince da matsayin fursunonin a kan siyasa da kyautata zaman rayuwarsu a cikin gidan kurkuku. Alan Garcia ya aika da sojoji zuwa wuraren domin 'maido da bin doka da oda'. A shekarar 1987, gwamnatin Alan Garcia ta mayar da bankuna na jama'a da su zama na gwamnati, wannan ya gamu da adawa mai tsanani. Ban da wannan kuma, domin gudanar da manufofinsa na tattalin arziki, Alan Garcia ya yi gyaran majalisar ministoci ta kasar Peru.
A cikin babban zaben shugaban kasa a wannan karo, Alan Garcia ya sami nasara, sabo da haka yana fuskantar kalubale cikin shekaru 5 masu zuwa. A cikin yakin neman zaben, ya taba bayyana cewa, ya riga ya san kuskure da ya yi a da, amma yana da kwarrewar gyaran kuskure da ya yi a da.
A halin yanzu, Alan Garcia ya yi shekaru 57 da haihuwa, kuma ya rubuta litattafai na adabi da yawa.(Danladi)
|