Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 10:04:10    
Wasu labaru game da wasannin motsa jiki(29/06-05/07)

cri
Ran 4 ga wata bisa agogon wurin, a Dortmund na kasar Jamus, kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Italiya da Jamus sun kara da juna a cikin gasar kusa da ta karshe, a karshe dai kungiyar Italiya ta ci nasara da ci 2 ba ko daya. Wadannan kungiyoyi 2 ba su jefa kwallon zuwa ragar juna ba a cikin mintoci 90, a cikin lokacin da aka kara, kungiyar kwallon kafa ta Italiya ta jefa kwallaye 2 zuwa ragar kungiyar Jamus a mintoci 118 da mintoci 120, ta tabbatar da nasara a minti na karshe, ta shiga cikin gasar karshe da za a yi a ran 9 ga wata bisa agogon wurin. Za ta yi karawa da wadda za ta ci nasara a cikin gasar da ke tsakanin kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Faransa da Portugal.

An labarta a kwanan baya cewa, yanzu ana shirya gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta mata da za a yi a kasar Sin a shekarar 2007 lami lafiya. Shugaban hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta duniya wato FIFA Mr. Sepp Joseph Blatter ya kuma bayyana cewa, yana da amanar cewa, za a samu nasarar yin wannan muhimmiyar gasar wasan kwallon kafa ta mata. Za a yi wannan gasa a birnin Shanghai da sauran birane 4 na kasar Sin, inda kungiyoyi 16 za su yi takara da juna don neman cin kofin duniya.

Ran 3 ga watan Yuli bisa agogon wurin, a cikin gasa ta zagaye na 4 tsakanin mace da mace ta budaddiyar gasar wasan kwallon tennis ta Wimbledon, 'yar wasan kwallon tennis ta kasar Sin Li Na ta lashe 'yar wasan kasar Czech da cin 2 da 1, ta haka ta shiga cikin jerin fitattun 'yan wasa 8 a wannan gami, saboda haka ta sami sakamako mafi kyau da 'yan wasan kasar Sin suka taba samu a cikin muhimman gasanni 4 na wasan kwallon tennis na duniya.

Ran 3 ga watan Yuni, kungiyar wasan kwallon kwando ta kasar Sin ta ci tura a gasar da ta yi da kungiyar kasar Italiya da 55 da 78 a cikin gasa bisa gayyata ta wasan kwallon kwando tsakanin maza na kasashe 4 da aka yi a kasar Italiya, a karshe dai ta zama ta 3 a cikin wannan gasa. Kungiyar kasar Sin ta shiga wannan gasa ne don share fage ga gasar fid da gwani ta wasan kwallon kwando ta maza ta duniya da za a yi a karshen watan Agusta a kasar Japan.(Tasallah)