Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-05 09:42:40    
Kungiyoyin kwallon kafa na Latin Amurka sun gwada gwanintarsu a cikin gasar cin kofin duniya

cri
Yanzu gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa ta shekarar 2006 da ake yi a kasar Jamus ta kusan zuwa karshe. A cikin wannan gasar, kungiyoyin kwallon kafa na kasashen Latin Amurka kamarsu kungiyoyin kasashen Brazil da Argentina sun gwada gwanintarsu sosai.

Har zuwa ran 27 ga watan Yuni, dukan kungiyoyi 8 mafiya nagarta na wannan zagaye sun fito. Ko da yake, kungiyoyin kasashen Turai sun sami kujeru 6 daga cikin guda 8, amma kungiyoyin kasashen Argentina da Brazil sun fi ba da alama a cikin zukantan mutane. Sa'an nan kuma, kungiyar kasar Ecuador ita ma ta nuna rawar gani.

Kungiyoyin kasashen Brazil da Argentina sun dade suna nuna karfinsu a fannin wasan kwallon kafa a Kudancin Amurka, kungiyar Brazil ta taba cin kofin duniya har sau 5, kungiyar Argentina ma ta ci kofin duniya sau 2. A wannan gami, kungiyar Brazil ta ci nasara a cikin dukan gasanni 3 na zagaye na farko, daga baya ta lashe kungiyar kasar Ghana da ci 3 ba ko daya.

Amma kungiyar Argentina ta fi nuna rawar gani, in an kwatanta da kungiyar Brazil. Ta zama ta farko a cikin rukuni na C, ta nuna babban karfinta na jefa kwallo zuwa ragar abokan karawa. Wakilin 'jaridar wasannonin motsa jiki ta birnin Mexico' Mr. Pepe Rodriguez ya nuna wa kungiyar Argentina babban yabo, ya ce,'kungiyoyin kasashen Brazil da Argetina sun dade suna nuna gwanintarsu, idan sun shiga gasanni na zagaye na karshe, to, wannan ba abin mamaki ba. Amma kungiyar Argentina ta faranta mana rayuka saboda fasaharta da dabararta da kuma taimakon juna da 'yan wasanta suka yi a cikin gasa.. Har kullum dukansu suna da damar shiga cikin gasanni na karshe.'

Ban da wannan kuma, makin da kungiyar Ecuador ta samu a wannan gami ya jawo hankulan mutane. Ta shiga cikin jerin fitattun kungiyoyi 16. Mr. Rodriguez ya kara da cewa,'kungiyar da ta fi ba da mamaki a wannan gami ita ce kungiyar Ecuador. Na kan mai da hankali kanta kullum. Hanyoyin da take bi wajen yin gasa sun sha bamban da wadanda aka saba bi. Tana da saurin musayar kai hari daga yin tsaro da kuma saurin kai hari. Ina tsammani cewa, dalilin da ya sa haka shi ne saboda ta kan yi karawa da kungiyoyin kasashen Chile da Paraguay, wadanda suka fi nuna gwaninta wajen sauri da karfi, shi ya sa, wannan ya kara mata sabbin abubuwa a cikin dabarun wasan kwallon kafa. Hanyoyi masu amfani kuma na ba zata da kungiyar Ecuador ke bi sun kawo mata nasara.'

Ban da wadannan kungiyoyi 3, kungiyar Mexico ita ma ta yi fintikau a cikin wannan muhimmiyar gasa.

A cikin gasar cin kofin duniya da ake yi, kungiyoyin kasashen Latin Amurka su ma sun nuna halin musamman na fasaha da dabarar karawa, wadanda suka nuna bambanci da na da. Kwararren wakili mai ilmin wasan kwallon kafa na gidan rediyon Caracol ta kasar Columbia Mr. Jose Parra yana ganin cewa,'yanzu ban sa ran alheri kan kungiyar kasar Brazil ba. Ko da yake tana da karfi, amma sun yi karancin ra'ayin daidaita kalubale. Na fi son kungiyar kasar Argentina. Tana da kwarewa a dukan fannoni, haka kuma, ta yi iyakacin kokarinta don neman cin nasara. Dukan wadannan kungiyoyi 2 wakilai ne na kungiyoyin wasan kwallon kafa na Latin Amurka, daga wajensu kuma, mun iya gano cewa, salon wasan kwallon kafa da kasashen Latin Amurka ke bi ya canja sosai, sun fi dora muhimmanci kan sauri da taimakon juna. Babban dalilin da ya sa haka shi ne saboda 'yan wasa masu yawa na wadannan kasashe 2 sun yi aiki a cikin kungiyoyin kwallon kafa na Turai, sun komar da ra'ayoyi da dabaru da yawa na Turai zuwa gida, daga baya, an yada wadannan ra'ayoyi da dabaru zuwa sauran kasashen Latin Amurka ta hanyar hadaddun gasannin wadannan kasashe 2.'(Tasallah)