A ran 4 ga wata a nan birnin Beijing, gwamnatin kasar Sin ta sanar da cewa, za ta fara tafiyar da "Shirin hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin kasashen duniya kan magungunan gargajiya na kasar", kuma ta yi kokarin kafa wani dandalin hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya a wannan fanni, da aiwatar da albarkatun kimiyya da fasaha na duk duniya domin ciyar da yunkurin mai da magungunan gargajiya na kasar Sin daidai da zamani gaba, ta yadda za a mai da irin wadannan magunguna su zama muhimmin karfin kawo zaman alheri ga lafiyar dan adam. To, jama'a masu sauraro, yanzu za mu karanta muku wani bayanin da wakilinmu ya ruwaito mana kan wannan labari.
Yau kafin shekaru fiye da 3000 ke nan da aka fara hada magungunan gargajiya na kasar Sin, muhimmin aikin da aka yi shi ne an yi amfani da saiwoyin tsimi na halitta domin kawar da cuce-cuce, ya kasance da cikakken tsarin hasashe da hakikanan aikatawar da aka yi cikin dogon lokaci, wannan ya samo sha'awa daga jama'ar Sin sosai. Cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, magungunan gargajiya na kasar Sin suna ta kara barbazuwa da jawo tasiri ga kasashen duniya a kowace rana, an riga an fitar da irin wadannan magunguna zuwa kasashe da shiyyoyi 135 na duniya, yawan daliban da suke koyon ilmin magungunan gargajiya na kasar Sin sai kara karuwa suke. Amma sabo da bambancin da ke akwai wajen al'adu da tarihi da addini, shi ya sa har ila yau kimiyyar tsarin hasashen magungunan gargajiya na kasar Sin ba ta samu karbuwa daga wajen dukkan mutanen duniya ba tukuna, kuma amfanin da irin wadannan magungunan suka bayar wajen rin rigakafi da kawar da cuce-cuce na zamani da sa kaimi ga lafiyar mutane bai bayyanu sosai ba.
Daidai bisa irin wannan hali ne, gwamnatin kasar Sin ta kaddamar da "Shirin hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin kasashen duniya kan magunguna gargajiya na kasar", wato ta hanyar yin hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin kasashen duniya ne, za a shigo da kwararru da kimiyya da fasaha da kudi da basira da kuma labaru daga duk duniya baki daya domin arzuta da kuma bunkasa hasashen magungunan gargajiya na kasar Sin, ta yadda za a yi amfani da irin wadannan magunguna domin kyautata sha'anin kiwon lafiya na duk 'yan adam.
Bisa bayanin da Mr. Li Daning, mataimakin shugaban ofishin kula da magungunan gargajiya na kasar Sin ya bayar an ce, wannan ne karo na farko da gwamnatin kasar Sin ta ba da shawarar tsara shirin hadin gwiwar kimiyya da fasaha tsakanin kasashen duniya bisa babban mataki kamar haka. Ya ce, "Daga wani fanni ya kamata mu daga matsayin hada magungunan gargajiya na kasar Sin da kara ingancinsu ta hanyar yin amfani da fasahar zamani, da tabbatar da manufar zamanintarwa wajen yin wadannan magunguna, daga wani fanni daban kuma ya kamata mu yi amfani da sakamakon da aka samu wajen fasahar binciken ilmin abubuwa masu rai da na magungunan zamani, da fasahar zamani da ma'aunin kasashen duniya da kowa ya amince, kuma a kirkiro tare da kago sabbin magunguna bisa harsashen magungunan jirgajiya na kasar Sin, ta yadda za a sa kaimi ga bunkasa sana'ar hada magunguna na zamani".
Mr. Jin Xiaoming, shugaban hukumar hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya ta ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ya ce, "Ma'aikata kimiya da fasaha za ta ware kudin Yuan miliyan 100 a wannan shekara domin yin ayyuka guda 50 na hadin gwiwar kimiyya da fasaha a tsakaninta da kasashen duniya da kuma M.D.D. kan wannan fanni." (Umaru)
|