A ran 3 ga wata, yayin da yake zantawa da manema labarai na Amurka, Nicholas Burns, mataimakin sakatariyar harkokin waje mai kula da harkokin siyasa na kasar Amurka ya bayyana cewa, idan kasar Iran ba ta mayar da martani ga shirin da kasashe shida suka gabatar kafin ran 12 ga wata, to kasar Amurka za ta nemi daukar matakai ga kasar Iran ta MDD.
Kuma Nr. Burns ya bayyana cewa, ran 12 ga wata wata muhimmiyar rana ce, sabo da a wancan rana, sakatariyar harkokin waje ta Amurka Madam Rice za ta yi shawarwari tare da ministocin harkokin waje na kasashen Rasha da Sin da Faransa da Birtaniya da kuma Jamus domin yin tattaunawa kan batun nukiliya na kasar Iran. Ban da wannan kuma ya ce, idan kasar Iran ba ta mayar da martani ga shirin da kasashe shida suka gabatar kafin ran 12 ga wata, to za ta karbi babban matsi daga kasashen duniya. Yanzu akwai hanyoyi biyu da ke gaban kasar Iran, daya shi ne yin shawarwari, dayan kuwa shi ne fuskatar matakan da kwamitin sulhu na MDD zai dauka.(Kande Gao)
|