Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-03 19:06:02    
Gwamnatin kasar Sin za ta kara horar da kwararrun mutane

cri

Yanzu, kamfanoni da masana'antu da yawa na kasar Sin suna fuskantar maganar karancin kwararrun mutane, wadda ta kawo cikas ga yunkurin yalwata su. Wannan magana ta rigaya ta jawo hankalin da'irori daban daban na al'ummar kasar Sin. Gwmnatin kasar Sin ita ma ta riga ta fito da manufofin da abun ya shafa game da yadda za a horar da kwararrun mutane.

Ma'aikatar kera na'ura ta farko ta Beijing, wani kamfani ne dake kera na'urorin zamani. Jimlar darajar kudin da yakan samu a kowace shekara ta kai kudin kasar Sin wato Renminbi Yuan biliyan daya. Mr. Zhu Bing, shugaban ma'aikatar kula da albarkatun kwadago ta kamfanin ya furta, cewa kodayake 'yan kwadago dake cikin kamfanin sun kai kusan 2,000, amma kamfanin na fuskantar maganar karancin kwararrun mutane a wani fannin sana'a ta musamman. Mr. Zhu Bing ya fadi, cewa :

'Da yake kamfaninmu ya samu bunkasuwa da saurin gaske, shi ya sa yake karancin kwararrun mutane kwarai da gaske, wadanda suke da ilmin kera na'urori na zamani da kuma sarrafa su da kyau. Lallai wannan magana ta hana ci gaban kamfanin a nan gaba'.

A halin yanzu, akwai kamfanoni da masana'antu da yawa dake karancin kwararrun mutane kamar yadda ma'aikatar kera na'ura ta farko ta Beijing take a kasar Sin. Wadannan kamfanoni da masana'antu suna kishin samun ma'aikata da injiniyoyi wato kwararrun mutane, wadanda suke da ilmi da fasahohi na musamman. Bisa kididdigar da aka yi, an ce a cikin ma'aikata masu aikin fasaha na kasar Sin, kalilan ne wato kashi 20 bisa kashi 100 daga cikinsu ne kawai suka samu takardun shaidar izni a fannin sana'o'i. Babu tantama, kasashe masu ci gaban masana'antu sun tafi sun bar kasar Sin baya a wannan fanni. Masana tattalin arziki sun bayyana, cewa wannan hali ya riga ya kawo cikas ga samun bunkasuwar tattalin arzikin al'ummar kasar Sin cikin dogon lokaci.

Dalilai guda uku ne suka haddasa maganar karancin kwararrun mutane. Dalili na farko, shi ne sassan da abun ya shafa na kasar Sin sun kasa mai da hankali cikin dogon lokaci kan horaswa a fannin sana'a, wato ke nan ba su zuba isasshen jari wajen bunkasa wannan fanni ba ; Dalili na biyu, shi ne kamfanoni da masana'antu na kasar sun nuna rashin kulawa da aikin horar da kwararrun mutane ; Dalili na uku wato na karshe, shi ne kwararrun mutane ba su samun lada gwargwadon aikinsu saboda ba a kafa tsarin sa kaimi da na kimantawa ba.

Game da wannan dai, a kwanakin baya ba da dadewa ba, gwamnatin kasar Sin ta fito da tsauraran matakai guda 9 na kara aikin horar da kwararrun mutane.

An bayyana, cewa wadannan matakai sun hada da batun horar da mutane a fannin sana'a ,da batun jarraba da kuma kimanta ayyukansu ,da batun ba da kudin yabo da kuma sa kaimi gare su da kuma batun ba da tabbaci ga zaman al'umma. Gwamnatin kasar Sin ta ba da shawarar sa kaimi ga dukkan kungiyoyin jama'a wajen gudanar da yunkurin horar da kwararrun mutane ,da kafa tsarin tattara makudan kudade daga gwamnatin kasar ,da kamfanoni da masana'antu da kuma kungiyoyin jama'a na kasar don horar da kwararrun mutane. Ban da wannan kuma, gwamnatin kasar Sin ta nemi gwamnatoci na matakai daban daban da su dora aikin horar da kwarrrun mutane cikin shirin bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar ; Mr. Zhang Bin, mataimakin shugaban sashen kula da harkokin horaswa na ma'aikatar kwadago da ba da tabbaci ga zaman al'ummar kasar Sin ya furta, cewa :

' Akwai abubuwa guda biyu da za a gudanar da su cikin gaggawa domin aiwatar da wadannan matakai. Abu na farko, shi ne gaggauta horar da dimbin kwararrun mutane na-gari kamar yadda ya kamata ; Abu na biyu da za a yi, shi ne a kafa sabon tsarin kyautata da kimanta da kuma sa kaimi ga kwararrun mutane, ta yadda mizanin 'yan kwadago masu aikin fasaha zai dace da yanayin bunkasa tattalin arziki da zaman al'ummar kasar'.

A karshe dai, Mr. Zhang Bin ya ce, ya zuwa shekarar 2010, kashi 40 cikin kashi 100 na ma'aikata masu aikin fasaha na kasar Sin za su zama kwararrun mutane.( Sani Wang )