Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-03 18:19:35    
An fara zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja a kan kololuwan duniya cikin tarihin dan adam

cri
A ran 3 ga wata da safe, karo na farko ne jirgin kasa na fasinja mai lamba T27 wanda ya tashi daga birnin Beijing zuwa birnin Lhasa ya ratsa kogon dutsen Kunlun mai tsawon mita 1668 kuma mai daskarariyar kasa. Wannan ya zama jirgin kasa na fasinja na farko da ke tafiya kan tsaunuka masu fadi na Qinghai-Tibet bayan bikin murnar bude hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet da aka yi yau da kwanaki 2 da suka wuce. Daga nan ne aka bude tarihin zirga-zirgar jiragen kasa na fasinja a kan kololuwan duniya.

Kwararru sun kimanta cewa, wannan hanyar dogo mafi tsowo da aka shimfida akan tsaunuka mafiya tsayi daga leburin teku zai dauki nauyin kashi 75 bisa 100 na sufurin kai da kawowa a tsakanin jihar Tibet da sauran wurare. (Umaru)