A ran 2 ga wata, an rufe taron shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka na 7 da aka shafe kwanaki 2 ana yinsa a birnin Banjul na kasar Gambiya. A gun taron, an bayar da wata takarda cewa, kasashen Afirka suna da niyyar kara saurin raya Afirka bai daya.
A gun bikin kaddamar da taron, Mr. Alpha Oumar Konare, shugaban kwamitin kungiyar Tarayyar Afirka ya jaddada cewa, idan ba a iya raya Afirka bai daya ba, shi ke nan, ana da wuyar kara saurin ci gaban Afirka. Sabo da haka, wakilan kasashe daban-daban wadanda suka hallara a gun taron sun tattauna kuma sun yi muhawara sosai kan batutuwan yadda za a raya fasahohin sadarwa da IT da ayyukan samar da wutar lantarki da zirga-zirgar jiragen kasa da ta jiragen sama, sun kuma sami ra'ayi daya kan batutuwa da yawa. Game da batun raya fasahohin sadarwa da IT a Afirka, a cikin yarjejeniyar ka'idojin raya fasahohin sadarwa da IT a Afirka da suka daddale a ran 2 ga wata, wakilan kasashe daban-daban da suka halarci taron sun nemi kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Afirka da su cika alkawuran kara saurin raya sana'ar sadarwa. Bisa wannan yarjejeniya, kwamitin kungiyar Tarayyar Afirka zai sa ido da ba da jagoranci ga kasashen da ke cikin kungiyar wajen neman bunkasuwar sana'ar sadarwa. Kasashen da ke cikin kungiyar Tarayyar Afirka ma za su kara yin hadin guiwa a tsakaninsu wajen ci gaban fasahohin sadarwa a nahiyar Afirka. Sannan kuma, an zartas da wani kuduri, inda aka nemi kasashen Afirka da su kara raya ayyukan yau da kullum, ciki har da ayyukan zirga-zirga da samar da albarkatun halitta da na samar da wutar lantarki domin ciyar da yunkurin raya Afirka na bai daya zuwa gaba.
Bugu da kari kuma, a gun taron, an yi kira ga kasashen kungiyar Tarayyar Afirka da su cika alkawarin sa aikin raya ayyukan samar da wutar lantarki a kan gaban dukkan aikace-aikacen da suke yi. Kwamitin kungiyar Tarayyar Afirka zai dauki matakai iri iri da suka wajaba, kuma zai sa kaimi kan kwamitin tattalin arzikin Afirka na M.D.D. da bankin raya Afirka da kwamitin albarkatun halitta na Afirka kuma da kungiyoyin hada kan tattalin arziki da su kara yin hadin guiwa wajen aiwatar da shirin raya sana'ar samar da wutar lantarki.
Ban da batun raya Afirka bai daya, wakilai wadanda suka halarci taron sun tattauna kuma sun sami ra'ayi daya kan batutuwan shiyyar Darfur na Sudan da na halin da ake ciki a kasar Somaliya. Game da batun Darfur na Sudan, Nkosazana Dlamini Zuma, shugabar kwamitin sulhu na kungiyar Tarayyar Afirka kuma ministar harkokin waje ta kasar Afirka ta kudu ta bayyana cewa, idan an yi shawarwarin neman zaman lafiya a tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawaye na Sudan lami lafiya, za a janye jikin sojojin kungiyar Tarayyar Afirka wadanda suke tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur daga kasar Sudan kafin ran 30 ga watan Satumba na shekarar da muke ciki, wato karshen lokacin wa'adin aikin tabbatar da zaman lafiya. A waje daya kuma, madam Zuma ta bayyana cewa, kungiyar Tarayyar Afirka za ta sa takunkumi kan wadanda suke yunkurin lalata yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya a shiyyar Darfur.
Game da batun Somaliya, wakilai sun yi fatan tun da wuri M.D.D. za ta soke takunkumin makamai da ta sa a kan kasar Somaliya. Sabo da haka, kungiyar neman bunkasuwa ta gwamnatocin kasashen gabashin Afirka za ta iya aikawa da sojojinta na tabbatar da zaman lafiya a kasar Somaliya.
Jama'a masu sauraro, abu daban da ya fi jawo hankulan mutane shi ne, shugaban kasar Iran Mahmoud Ahmadinejad da shugaba Hugo Chavez, shugaban kasar Venazuela sun kuma halarci wannan taron shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Afirka bisa gayyatar da aka yi musu. An bayar da labari cewa, a gun taron, Mr. Ahmadinejad ya gana da wasu shugabannin kasashen Afirka. Bayan da ya koma kasarsa, ya bayyana cewa, kasashen Afirka suna da fatan kulla dangantaka a tsakaninsu da kasar Iran daga duk fannoni. Sannan kuma, lokacin da ya bayar da jawabi a gun taron, Mr. Chavez ya yi kira ga kasashen Afirka da su yi yaki da tsarin danniya da ake son shimfidawa a duk duniya.
Ko shakka babu, domin kasashen Afirka ba su da niyya da karfin daidaita wani batu tare, sakamakon da aka samu a gun wannan taro ya yi kadan, musamman, ba a iya gabatar da shirin tsarin mulkin kungiyar Tarayyar Afirka ga wannan taron shuganninta ba. (Sanusi Chen)
|