Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-03 15:53:35    
An yi yawon shakatawa a kasar Massar

cri

Kasar Massar tana iyakar Asiya da Afirka, yammacinta shi ne kasar Libya, kudancinta shi ne kasar Sudan, gabashinta shi ne bahar Maliya da Palesdinu da Isra'ila, arewacinta shi ne Bahar Rum. Yawancin fadin kasar Massar yana arewa maso gabashin nahiyar Afirka, zirin Sinai da ke gabashin koramar Suez yana kudu maso yammacin nahiyar Asiya.

Tsawon gabar teku na kasar Massar ya kai kilomita dubu 2 da dari 9, amma Massar kasa ce mai hamada, sabo da fadin hamadar ya kai kashi 96 daga cikin dari na yankin kasar Massar.

Kogin Nail mafiya tsawo a duk duniya ya ratsa kasar Massar, tsawonsa ya kai kilomita dubu 1 da dari 3 da 50, yankin Delta da ke gabobin kogin Nail ya fi albarkatu a kasar Massar, ko da yake fadin yankin Delta ya kai kashi 4 daga cikin dari na kasar Massar, amma kashi 99 daga cikin dari na mutanenta suna zama a wannan yanki.

Koramar Suez ta hada nahiyar Turai da Asiya da Afirka, kuma ta hada bahar Maliya da Bahar Rum, haka kuma ta haka tekun Atlantic da na India, sabo da haka, tana da ma'ana sosai a kan manyan tsare tsare da tattalin arziki.

Yawan kasar Massar ya kai miliyan 71 da dubu 900, yawancinsu kuma Larabawa ne. Addinin musulunci ya kasance addinin kasa a Massar, 'yan kasar Massar su ne 'yan rukunin Sunni. Harshen gwamnatin kasar shi ne harshen Larabci. Babban birnin kasar Massar shi ne birnin Alkahira, yawan mutanen da ke zauna a wurin ya kai miliyan 7 da dubu 765, ta haka ya zama birnin da ke da mafi yawan mutane a kasashen Larabawa da ke nahiyar Afirka.

Kasar Massar tana da dogon tarihi, a cikin tarihinta, mutanen Polish da Girika da Roma da Larabawa da Turkiya sun taba mulki a kasar Massar. A karshen karni na 19, sojojin kasar Britaniya sun mallaki kasar. A ranar 23 ga watan Yuli na shekarar 1952, an kori mutanen waje 'yan mulkin mallaka. A ranar 18 ga watan Yuni na shekarar 1953, an kafa jamhuriyyar kasar Masssar, a shekarar 1971, an canza sunanta da ya zama jamhuriyya kasar Massar ta Larabawa.

Massar shahararriyar kasa ce daga cikin manyan kasashe hudu da ke da dogon tarihi da dadaddun al'adu, sabo da haka ana kiranta 'dakin ajiye abubuwan tarihi na duniya'. A yankin kogin Nail da bahar Rum da yammacin hamada, ana iya samun abubuwan tarihi da tsofaffin al'adu da yawa, wadanda suka hada da manyan zane zane da tsaunukan pyramid da gunki na sphinx, sabo da haka, kasar Massar ta zama wani shahararren wurin yawon shakatawa.

Kasashen Sin da Massar suna da zumunci na gargajiya. Kafin shekaru fiye da dubu 2, sun fara cudanya da juna. A watan Mayu na shekarar 1956, kasashen biyu sun kulla dangantakar diplomasiyya, ta haka ta zama kasa ta farko da ta amince da kasar Sin a cikin kasashen Larabawa da kasashen Afirka. Bayan da suka kafa dangantakar diplomasiyya, dangantakar abokantaka da gama kai tana kara samun bunkasuwa. A shekarar 1999, kasashen biyu sun kafa dangantakar gama kai bisa manyan tsare tsare a karni na 21, sabo da haka, dangantakarsu ta shiga cikin wani sabon mataki. A cikin 'yan shekarun baya, shugabannin kasashen biyu suna kara ganawa da juna, haka kuma suna kara gama kai a fannonin siyasa da tattalin arziki da kimiyya da fasaha da al'adu da dai sauransu. A cikin shekarar 2005, yawan kudin suka samu daga cinikayya ya kai dala biliyan 2 da miliyan 145, wanda ya karu da kashi 36.1 daga cikin dari bisa na makamancin lokaci.(Danladi)