Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-02 19:52:12    
Wurare 4 da ke gabobi 2 na kasar Sin sun girmama aikin fara zirga-zirgar jiragen kasa bisa hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet

cri
A ran 1 ga wata, an fara zirga-zirgar jiragen kasa bisa hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet wadda ta jawo hankulan kasashen duniya. Kafofin watsa labaru na wurare 4 da ke gabobi 2 na kasar Sin sun girmama wannan al'amari sosai.

A wannan rana, jaridar "People's Daily" mafi kwar jini ta kasar Sin ta buga wani bayanin edita cewa, aikin shimfida hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet babban buri ne na Sinawa 'yan zuriyoyi kadan, kuma babban kuduri ne da ya shafi batun bunkasa tattalin arziki da zaman al'umman kasar Sin.

A wannan rana kuma kafofin watsa labaru na Taiwan da na Hongkong da na Macao su ma sun yi jinjina sosai ga wannan al'amari.

Kafofin watsa labaru na Taiwan sun bayyana cewa, aikin fara zirga-zirgar jiragen kasa bisa wannan hanayar dogo zai jawo zarafin tarihi ga lardin Qinghai da jihar Tibet wajen bunkasa tattalin arziki da zaman al'umma.

Wata jaridar Hongkong ta bayyana cewa, sassan sana'ar yawon shakatawa na Hongkong sun sa ran alheri cewa, bayan da aka faran zirga-zirgar hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet, yawan mutanen Hongkong da za su je Tibet domin yawon shakatawa zai karu da fiye da kashi 20 bisa 100.

Wata jaridar Macao kuma ta buga wani bayani cewa, bisa bunkasuwar da za a samu wajen zirga-zirga da sufuri ta hanyar dogo ta Tibet, ba shakka musanye-musanye da kai da kawowa da za a yi a tsakanin jihar Tibet da makwabtan kasashen da ke kudu mato yammacin kasar Sin za su karu-karuwar gaske. (Umaru)