 A ran 1 ga watan Yuli, an fara zirga-zirgar jiragen kasa bisa hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet, wadda ta zama hanyar dogo mafi tsawo da aka shimfida kan tsaunuka masu fadi kuma mafi tsayi daga leburin teku na duniya. Kafofin watsa labaru na kasashen waje sun sa lura sosai kan wannan al'amari.
A ran 2 ga wata, muhimman jaridu daban-daban na kasar Thailand dukkansu sun buga labari game da fara aiki da wannan hanyar dogo a saman shafi na farko, kuma sun nuna babban yabo cewa, "wannan ya zama kagowa ce cikin tarihin hanyoyin dogo".
A ran 1 ga wata, jaridar "Reform" wadda ta fi bugawa ta 2 ta Mexico ta buga cikakken bayani game da hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet, kuma ta tsamo maganar da shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya fada cewa, "wannan ba babbar kagowa cikin tarihin shimfida hanyoyin dogo na kasar Sin kawai ba ce, haka kuma wani babban abin al'ajibi ne cikin tarihin hanyoyin dogo na duniya."
Cikin bayanin da jaridar La Repubbilica" ta Italiya ta buga a ran 1 ga wata ta bayyana cewa, kasar Sin wadda dake cikin karni na 21 ta samu nasara kan kalubalen da aka yi mata ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha na zamani. (Umaru)
|