Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-02 09:23:45    
Jirgin kasa na farko ya isa tashar Lhasa ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet

cri

A ran 2 ga wata da asuba, agogon Beijing, jirgin kasa na farko da ya tashi daga birnin Germu na lardin Qinghai zuwa birnin Lhasa na jihar Tibet mai cin gashin kanta ta hanyar dogo ta Qinghai-Tibet ya isa tashar Lhasa lami lafiya. Sannan kuma, da karfe sifiri da minti 13 na ran 2 ga wata, jirgin kasa daban da ya tashi daga tashar Lhasa ta jihar Tibet zuwa tashar Germu ta lardin Qinghai ya kuma isa birnin Germu lami lafya. Wannan ya almantar da cewa an fara kaddamar da hanyar dogo ta Qinghai-Tibet.

Jirgin kasa da ya tashi daga birnin Germu a ran 1 ga wata da safe kuma ke da fasinjoji fiye da dari 6 ya isa tashar Lhasa bayan da ya sha tafiye-tafiye har na tsawon sa'o'i 13 a kan hanyar dogo ta Qinghai-Tibet da tsawonta ya kai kilomita 1142. Wannan jirgin kasa ya ratsa tudun Qinghai-Tibet, wato kololuwar tsaunukan duniya. (Sanusi Chen)