 Yau an kaddamar da duk hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin. Wurare daban daban na kasar Sin sun darajanta wannan.
Jaridar People Daily za ta ba da bayani don taya murnar kaddamar da hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin.
Bayanin ya bayyana cewa, gina hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin buri ne da jama'ar kasar Sin suka dade suna neman cimmawa zuriya bayan zuriya, haka kuma, babban kuduri ne da ke da nasaba da bunkasuwar zaman al'umma da tattalin arzikin kasar Sin sosai. Wahaloli da kalubalen da aka fuskanta a lokacin shimfida wannan hanya wadanda ba a taba fuskanta ba a tarihin shimfida hanyoyin jiragen kasa na duniya. Masu shimfida hanyar jirgin kasa sama da dubu dari sun haye wahaloli iri daban daban, sun shimfida hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet a babban tudu, sun nuna 'ra'ayin na shimfida hanyar jirgin kasa iri ta zamani da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet' wajen magance kalubalen da ake fuskanta a fannin lafiyar jama'a. Irin wannan ra'ayi ya zama babban kwarin gwiwa ne da aka bai wa mutanen kasar Sin biliyan 1 da miliyan 300 wajen neman samun ci gaba ba tare da kasala ba.(Tasallah)
|