Jaridar Macao daily ta bayar da bayanin edita a yau 1 ga wata cewa, hanyar jirgin kasa da ke tsakanin lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin wadda aka fara aiki da ita a ran nan ta bude wani sabon zamani na samun bunkasuwar zaman al'umma da tattalin arziki daga dukan fannoni kuma cikin kwanciyar hankali a jihar Tibet wadda ke kudu maso yammacin kasar Sin.
Bayanin yana ganin cewa, kafin an fara aiki da wannan hanyar dogo, jihar Tibet jiha ce da babu hanyoyin jirgin kasa, wannan ya dakatar da cudanyar Tibet da sauran wurare. Fara aiki da wannan hanyar jirgin kasa da aka yi, zai kawo albarkar aikin yawon shakatawa a jihar Tibet, haka kuma zai sa kaimi ga kara cudanyar kabilu daban daban.(Lubabatu Lei)
|