Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-07-01 17:30:59    
An kaddamar da hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin

cri

A ran 1 ga wata, kasar Sin ta shirya gagarumin biki don murnar kammala aikin shimfida hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet ta kasar Sin. Wannan hanya wata hanyar jirgin kasa ce da aka gina a kan duwatsu mafi tsayi a duniya. Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya halarci wannan biki inda ya bayyana cewa, hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet wata babbar abar al'ajabi ce ga tarihin dan adam dangane da aikin shimfida hanyar jirgin kasa. Ya ce, "shimfida hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet buri ne da jama'ar Sin suka dade suna nema cimmawa zuriya bayan zuriya. Sa'an nan shimfida wannan hanya kalubala ce ga kasar Sin a fannin tattalin arziki da kimiyya da fasaha, kuma ga lafiyar dan adam. Ga shi yanzu an cimma buri da jama'ar Sin musamman jami'ai da fararen hula na wuraren hanyar suka dade suna nema zuriya bayan zuriya. Haka zalika ba ma kawai kammala aikin shimfida hanyar nan babban aikin bajinta ne ga tarihin kasar Sin na shimdida hanyar jirgin kasa ba, har ma babban abin al'ajabi ne ga tarihin duniya kan shimfida hanyar jirgin kasa."

Wannan hanyar jirgin kasa ta tashi daga birnin Xining, fadar gwamnatin lardin Qinghai a gabas zuwa birnin Lhasa, fadar gwamnatin jihar Tibet a yamma. Duk tsawonta ya kai kilomita 1956. An shimfida hanyar nan ne a kan manyan tsaunuka da matsakaicin tsayinsu ya wuce mita 4000 daga leburin teku. Tun can a shekarar 1984, an riga an fara aikin sashen farko na hanyar mai tsawon kimomita 814 da ya hada birnin Xining da na Ge'ermu. Ka zalika an fara aikin shimfida sashe na biyu na hanya mai tsawon kilomita 1142 da ya hada birnin Ge'ermu da na Lhasa a shekarar 2001.

Mutane da yawa suna jin matukar farin ciki da kaddamar da wannan hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet. Madam Ma Yumei, 'yar kabilar Hui wadda ke zama a birnin Ge'ermu ta ce, "ina farin ciki sosai da kadamar da wannan hanyar jirgin kasa. Yanzu, idan na dauki jirgin kasa daga garinmu na Ge'ermu zuwa birnin Lhasa, to, tafiyar za ta yi sauki kuma cikin sauri". Wani saurayi dan kabilar Han mai suna Yang Zengsen shi ma ya ce, "yana alla alla zai sami damar zuwa birnin Lhasa cikin jirgin kasa don yin yawon shakatawa. Yana sha'awar gane ma idonsa ni'imataccen hali na birnin Lhasa." Ya kuma bayyana ra'ayinsa cewa, za a ci gajiyar wannan hanyar jirgin kasa wajen bunkasa harkokin tattalin arziki a wurare da ta ratsa.

Daidai ne, a cikin jawabin da Mr Hu Jintao, shugaban kasar Sin ya yi a gun bikin murnar kaddamar da wannan hanyar jirgin kasa, ya ce, wannan hanyar jirgin kasa za ta samar da babbar dama ga lardin Qinghai da jihar Tibet da su kara samun bunkasuwa da sauri. Ya ce,

"kaddamar da hanyar jirgin kasa da ta hada lardin Qinghai da jihar Tibet yana da matukar muhimmanci ga gaggauta bunkasa harkokin tattalin arziki da na zamantakewar jama'a a wannan lardi da jiha, da kyautata zaman rayuwar jama'ar kabilu daban daban, da kara karfin hadin kansu, da kuma inganta ayyukan tsaron kasa. Ya kamata, lardin Qinghai da jihar Tibet su yi amfani da wannan dama wajen kafa tsarin bunkasa tattalin arziki bisa matsayinsu mai rinjaye. Su gina wurare da hanyar ta ratsa don su zama wurare masu ci gaban tattalin arziki da zaman jituwar jama'a da kuma kyakkyawan muhali." (Halilu)