A ran 29 ga wata, kotun koli ta tarayyar Amurka ta yanke hukunci cewa, gwamnatin Bush ta ba da umurnin kafa kotun soja ta musamman don yanke hunkunci kan fursunonin da ake tsare da su cikin kurkukun sansanin sojojin ruwa na Amurka da ke tsibirin Guantanamo na kasar Cuba, wannan danyen aikin da ta yi ya ketare ikonta, kuma ya keta dodokin shari'a na Amurka da dokokin kasashen duniya.
Bayan da aka samun sakamakon jefa kuri'u a wannan rana wato kuri'u 5 na goyon baya da 3 na ki, kotun koli ta Amurka ta yanke hukunci cewa, danyen aikin da gwamnatin Bush ta yi na ba da umurnin kafa kotun soja cikin kurkukun Guantanamo don yin shirin yanke hunkunci kan mutane 10 da aka zarge su ya keta dokokin shari'a na Amurka, kuma ya saba wa yarjejeniyar hakkin dan adam ta kasashen duniya ta Geneva.
Bayan farmakin ta'addancin da aka yi a ran "11 ga Satumba" na shekarar 2001, gwamnatin Bush ta fara shirin kafa kotun soja ta musamman don yanke hukunci kan fursunonin da ake tsare da su cikin kurkukun sansanin sojojin Amurka da ke tsibirin Guantanamo na kasar Cuba. Cikin fursunoni 450 da ake tsare da su yanzu cikin kurkukun Guantanamo, da akwai mutane 10 kawai wadanda suke fuskantar tuhumar da za a yi musu a gaban kotun soja, daga cikin su kuma har da Salim Ahmed Hamdan, dareban Osama Bin Laden, madugun kungiyar Al-Qaeda da ke kasar Afganistan.
Hamdan mai shekaru 36 da haihuwa wanda aka tsare shi cikin kurkukun Guantanamo har shakeru 4, wanda kuma aka kai masa kara bisa laifin da ya barkata daga shekarar 1996 zuwa ta 2001 na yin adawa da jama'ar Amurka kawai. Hamdan ya ki wannan kara, ya ce ya tuka mota domin Bin Laden ba don kome ba illa domin samun kudin zaman rayuwarsa ne kawai, wato aikin da ya yi ba wata hujja ba wani dalili. Lauya din Hamdan kuma ya yi tuhuma ga yawan ikon da aka ba wa gwamnatin Bush kan matsalar kafa kotun soja , ya ce Hamdan ya samu kiyayewa daga wajen "Yarjejeniyar Geneva", kuma ya kai kara ga kotun koli don neme ta da ta yanke hukuncin keta dokokin shari'a ga gwamnatin bush.
Kafofin watsa labaru na wurin sun bayyana cewa, hukuncin da kotun shari'a ta yanke ya zama wata babbar hasara ce ga gwamnatin Bush. Wani babban alkali ya ce, gwamnatin Bush ba ta da ikon daukar "matakin da ba safai akan gani irin sa ba" wato ta kafa kotun soja ta musamman don yanke hukunci kan mutanen da ake tuumarsu da laifin yin ta'addanci da ake tsare da su yanzu.
Bayan da aka ba da jerin labaru wulankancin da sojojin Amurka suke yi wa fursunoni, matsanancin halin da ake ciki a kurkukun Guantanamo ya kara gamuwa da la'anta daga wajen kasashen duniya. Wasu hukumomin da abin ya shafa na M.D.D. kulluma suna yin kira ga Amurka cewa, ko ta saki dukkan fursunonin da take tsare da su cikin kurkukun Guantanamo, ko kuma ta yanke musu hukunci, amma kada ta tsare su ba tare da kayyadadden lokaci ba.
Bisa halin haka, a kwanan baya Mr. Bush ya yi bayani cewa ya yi nufin rufe wannan kurkuku, amma ya ce dole ne da farko a tabbatar da yawan fursunonin da ya kamata a gurfanar da su a gaban kotu soja. Kotun koli na Amurka ta yanke wannan hukunci ne a ran 29 ga wannan wata a daidai bisa wannan halin da ake ciki yanzu.
Kafofin watsa labaru na Amurka sun sa lura cewa, hukuncin da kotun koli ta Amurka ta kanke ta shafi matsalar ko gwamnatin kasar tana da ikon kafa kotun soja ta musamman kawai, amma ba ta gabatar da muhimmiyar matsalar ko za a rufe kurkukun Guantanamo ba. (Umaru)
|