Jama'a, kun san cewa, tun cikin dogon lokaci, kungiyoyi masu karfi na kasashen Turai da na Amurka ta Kudu suna taka muhimmiyar rawa a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da aka saba yi sau daya a duk shekaru hudu. Amma lallai ba a tafi an bar kungiyoyin kasashen Asiya baya ba a 'yan shekarun baya, wato ke sun samu babban ci gaba wajen wasan. Gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006 da ake yi yanzu a kasar Jamus, ta zama tamkar wani ma'auni ne na gwada karfin da kungiyoyin kasashen Asiya suke da shi wajen buga kwallon kafa.
Lallai ba a manta ba, a gun gasar cin kofin duniya da aka yi a kasashen Korea ta Kudu da kuma Japan yau da shekaru 4 da suka gabata, kungiyoyin kasashen Asiya sun ba mutane mamaki domin kungiyar kasar Korea ta Kudu wato mai masaukin baki ta kafa tarihi har ta samu damar shiga cikin jerin kungiyoyi hudu masu karfi. Wannan ya zama sakamako mafi kyau da wata kungiyar Asiya ta samu a gun gasar cin kofin duniya; Kungiyar kasar Japan ma ta sami damar shiga cikin jerin kasashe dake kan matsayin gurabe 16 na farko a duniya a gun gasar.
Ga shi yanzu ana nan ana gudanar da gasar cin kofin duniya ta 18 ta wasan kwallon kafa a Turai. Abun bakin ciki, shi ne dukkan kungiyoyin kasashen Asiya sun sha kaye daga hannun abokan karawarsu, wato ba su samu damar shiga wasanni na zagaye na biyu ba. Amma duk da haka, Jagoran kungiyar wakilan kasar Iran Mr. Sahrukhi Homallon ya bayyana ra'ayinsa, cewa:' A ganina, kungiyoyin kasashen Asiya sun yi rawar gani a gun gasar. Ko da yake dukansu sun sha kaye daga hannun abokan karawarsu, amma sun nuna himma da kwazo wajen buga kwallo. Abun bakin cikin, shi ne ba su yi sa'a ba lokacin da suke saka kwallo a gidan abokan karawarsu.'
1 2
|