|
|
|
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye | more>> |
|
|
|
|
|
|
|
(GMT+08:00)
2006-06-30 10:42:52
|
Kungiyar kasashe 8 tana bukatar warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar siyasa
cri
Ran 29 ga wata a gun taron ministocin harkokin waje na kungiyar kasashe 8 da aka shirya a birnin Moscow, an bayar da wata sanarwa cewa, kungiyar kasashe 8 tana ta tsayan kan warware matsalar nukiliya ta kasar Iran ta hanyar siyasa. Sanarwar tana ganin cewa, daddale wata yarjejeniya mai dorewa a dukan fannoni, ba kawai zai sanya jama'ar kasar Iran su yi amfani da makamashin nukiliya ba, har ma zai kawo moriya mai dorewa wajen siyasa da tattalin arziki ga kasar Iran.
Sanarwar ta ce,kungiyar kasashe 8 sun nuna amincewa ga shawarwarin da Ali Larijani, sakataren kwamitin tsaron kasar Iran, da Javier Solana, babban wakilin tarayyar kasashen Turai mai kula da harkokin waje da manufar kwanciyar hankali za su yi a ran 5 ga watan Yuli, tana fata kasar Iran za ta ba da hakikanin amsa. (Bilkisu)
|
|
|