Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-29 15:49:48    
Kasar Sin za ta yi kokarin kiyaye muhallin hanyar jirgin kasa dake hada lardin Qinghai da jihar Tibet

cri

Wani labarin da wakilin rediyon kasar Sin ya rubuto mana ya bayyana cewa, a ran 29 ga watan nan da muke ciki, a nan birnin Beijing, wani jami'I na ma'aikatar kula da hanyoyin jirgin kasa na kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin za ta yi kokarin aiwatar da ayyukan kiyaye muhallin hanyar jirgin kasa dake hada lardin Qinghai da jihar Tibet.

A gun taron gana da maneman labaru da aka shirya a ofishin watsa labaru na majalisar gudanarwa ta kasar Sin, wannan jami'I ya yi furucin nan.

Wannan jami'I ya ci gaba da cewa, bayan da za a bude hanyar jirgin kasar dake hada lardin Qinghai da jihar Tibet, wasu sassan da abin ya shafa za su sa lura sosai ga muhallin hanyar nan da dabobbin daji da za su ketare a wurin nan. Bugu da kari kuma za a yi kokarin dauka matakai daban daban don kiyaye muhallin nan.(Dije)