An labarta, cewa jiya ranar Laraba, an kammala aikin gwajin dukkan na'urorin tashar jirgin kasa ta Lhasa ,wato tashar karshe ta hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet na kasar Sin. A sa'i daya kuma, an bude hanyar mota daga wannan tasha zuwa cibiyar birnin Lhasa, wato ke nan an soma aiki a hukunce da tashar jirgin kasa ta Lhasa.
Tashar jirgin kasa ta Lhasa tana kudancin yankin birnin Lhasa, wanda tsawonsa daga bakin teku ya wuce mita 3,600; Tashar nan tasha ce mafi girma dake jigilar kayayyaki da daukar fasinjoji a kan duk tsawon hanyar dogo da ta hada Qinghai da Tibet. Domin samar da sauki ga fasinjoji, an hauda lifta cikin dakunan tashar; kuma an yi amfani da makamashin rana wajen dumama dakunan tashar domin kiyaye muhallin wuraren dake kewayen tashar. ( Sani Wang )
|