Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-29 12:13:48    
Kasashen Afrika sun kara karfin gina tashoshin jiragen ruwa

cri
Tashoshin jiragen ruwa suna da muhimmanci wajen bunkasuwar tattalin arziki ta kasashen Afrika, amma yawancin kasashen Afrika sun rasa ci gaban gine-ginen tashoshin jiragen ruwa sosai. Bisa bunkasuwar tattalin arziki na Afrika, da kuma karuwar gasa a tsakanin tashoshin jiragen ruwa na kasashe daban daban, gwamnatocin kasashen Afrika daban daban sun dauki manufar zama kansa, da kuma sa himma domin jawo jari daga kasashen waje, sun yi gyare-gyare ga tashoshin jiragen ruwa ta hanyoyin jawo sabon tsarin gudanarwa, da kara zuba jari kan gine-gine, da dai sauransu, haka kuma sun kara karfin gine-ginen tashoshin jiragen ruwa.

Kasar Nijeria, babbar kasa da ke yammacin Afrika wajen tattalin arziki ta shirya yin gyare-gyaren zaman kansa ga tashoshin jiragen ruwa, domin kara amfanin jigila. Gwamnatin kasar Niejeria ta mika ikon gudanarwa ga masana'antu da kungiyoyi masu zaman kansu, bisa sharadin mai da ikon mallaka a karkashin shugabancin kasar. Gwamnatin kasar tana fatan jawo tsarin takara ta wadannan hanyoyi. A watan Afril, hukumar gudanarwar masana'antun kasar Nijeria ta mika ikon gudanarwa na wasu kwantena ga masana'antu masu zaman kansu daban daban, wannan ya nuna cewa, aikin gyare-gyaren zaman kansu na tashoshin jiragen ruwa na kasar Nijeria ya riga ya dauki wani hakikanin mataki.

Kasar Gana da ke yammacin Afrika ta kuma ta kara gaggauta gine-ginen tashoshin jiragen ruwa. A da, birnin Abidjan na kasar Cote Di'lvoire da ke makwabtaka da kasar Gana ya taba zama wani muhimmin birnin da ke bakin teku na shiyyar Afrika ta yamma, amma sabo da tasirin da yakin basasa na kasar ke kawo masa, matsayi da amfaninsa ya ragu sosai. Kasar Gana ta kama wannan dama, ta sabunta gine-ginen tashoshin jiragen ruwa na kasar, domin kara amfanin tashoshin jiragen ruwa.

A cikin kungiyar tarayyar bunkasuwar Afrika ta kudu da ta kunshi kasashe 14, manyan tashoshin jiragen ruwa na kasar Afrika ta kudu suna da amfani sosai, wajen jigilar yawancin kayayyaki na shiyyar. Amma, bisa karuwar tattalin arziki da ciniki ta shiyyar, tashoshin jiragen ruwa na kasar Afrika ba su da isasshen karfi wajen jigilar da kayayyaki. Ko da ya ke gwamnatin kasar Afrika ta kudu ba ta aiwatar da manufar zaman kansu ba, amma gwamnatin kasar tana kara zuba jari wajen gine-ginen tashoshin.

A shiyyar da ke arewacin Afrika, kasar Masar tana ci gaba da kai matsayin fifiko wajen habaka gine-ginen tashoshin jiragen ruwa. Ban da yin gyare-gyare ga wasu tashoshin jiragen ruwa, gwamnatin kasar Masar ta kuma kafa sababbin tashoshin.

A shekarar 2000, wata kungiyar tashar jiragen ruwa ta Hejihuangpu ta hongkong ta kasar Sin ta daddale wata yarjejeniya da gwamantin kasar Tanzania, wato ta samu ikon gudanarwa na wani kwantena na tashar jiragen ruwa ta Dares Salaam tare da wani kamfanin kasar. Bayan da suka samu ikon gudanarwa, kungiyar tashar Hejihuangpu ta zuba jari domin sabunta gine-gine, da kuma kawo tsarin gudanarwa mai zamani.

Sabo da karuwar karfin tashar jiragen ruwa ta Dares Salaam, tashar jiragen ruwa ta Mombasa ta kasar Kenya, wato muhimmiyar takararta ta ga tilas ne ta zuba kudi da yawa domin sabunta gine-gine, da kara amfaninta, domin ci gaba da kan matsayinsa na fifiko.

Kwararru sun nuna cewa, bisa karuwar bukatun albarkatu na Afrika da kasashen duniya suka yi, cinikin Afrika zai samu ci gaba, amfanin tashoshin jiragen ruwa wajen tattalin arzikin Afrika zai karu a kwana a tashi, sabo da haka, kasashe daban daban na Afrika za su kara saurin zuba jari da gine-ginen tashoshin jiragen ruwa. Amma, kasashen Afrika za su yi kokari sosai, idan suna fatan kafa manyan tashoshin jiragen riwa masu amfani sosai.