Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na IRNA na kasar Iran ya bayar a ran 28 ga wata, an ce, babban wakilin kungiyar EU mai kula da manufofin diplomasiyya da zaman lafiya Javier Solana zai kai ziyara a kasar Iran a makon gobe, haka kuma zai yi shawarwari da jami'an kasar Iran a kan sabon shirin da kasashe 6 suka gabatar da shi domin warware matsalar nukiliya ta kasar Iran.
An ce, Mr Solana ya kai wannan ziyara ne a madadin kungiyar EU da zaunannun mambobin kwamitin sulhu na MDD ciki har da kasar Amurka. Mr Solana ya ce, a gun ziyararsa zai kara karfafa matakai da aka dauka a kan tattalin arziki domin sa kaimi ga kasar Iran da ta karbi sabon shirin.(Danladi)
|