Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 16:14:27    
Dakin karatu na kasar Sin

cri

Masu sauraro, yanzu lokaci ya yi da za mu amsa tambayoyin masu sauraro. Tambayar da za mu amsa a cikin shirinmu na yau ta fito ne daga hannun mai sauraronmu Ahmad Ilyasu Bawa, mazauni Garki Abuja na kasar Nijeriya. Ya rubuto mana cewa, ina son a ba ni tarihin dakin karatu mafi girma a kasar Sin, kuma yawan littattafan da ke akwai da na'urorin da ke akwai a wannan dakin karatu? To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, bari mu yi muku takataccen bayani a kan dakin karatu na kasar Sin, wato dakin karatu da ya fi girma a nan kasar Sin.

Dakin karatu na kasar Sin asalinsa shi ne dakin karatu na Jingshi. A farkon karni na 20, a yayin da ake kokarin gyare-gyare don neman kara karfin kasa da koyon fasahohin kasashen yammacin duniya a nan kasar Sin, wasu masu hangen nesa sun yi kokarin shawartar gwamnatin daular Qing da ta kafa dakin karatu, don karfafa al'adun al'umma da kuma shigo da ilmin kimiyya na zamani. Sabo da haka, a shekara ta 1909, sarki Xuantong ya amince da kafa dakin karatu na Jingshi. A shekara ta 1929, an hade shi da dakin karatu na Beihai. Daga baya, a shekara ta 1931, an gama kafa sabbin harabobinsa a titin Wenjin, sabo da haka, ya zama dakin karatu da ya fi girma da kuma samun ci gaba a kasar Sin a wancan lokaci.

Bayan da aka kafa jamhuriyar jama'ar kasar Sin, sakamakon bunkasuwar kasa da kuma karuwar bukatun al'umma a fannin al'adu, ko da yake an yi ta habaka harabobin wannan dakin karatu, amma duk da haka, ba a cimma biyan bukatun jama'a ba. Sabo da haka kuma, a shekara ta 1975, marigayi Zhou Enlai, wanda ya kasance firaminista na farko na jamhuriyar jama'ar kasar Sin, ya ba da shawarar gina sabbin harabobin dakin karatu na Beijing, an kuma kammala wannan aiki a shekara ta 1987. A shekara ta 1998 kuma, an sake sunan wannan dakin karatu zuwa dakin karatu na kasar Sin.

Littattafai iri iri masu yawan gaske ne da ke akwai a cikin dakin karatu na kasar Sin, ciki har da na da da na yanzu da na gida da kuma na waje. Ya zuwa karshen shekara ta 2003, yawan littattafai da wannan dakin karatu ke da su ya riga ya kai miliyan 24 da dubu 110, wanda ya zo na biyar a tsakanin dakunan karatu na matsayin kasa na duk duniya, kuma adadin nan yana karuwa bisa dubu 600 zuwa dubu 700 a ko wace shekara.

Jerin littattafai mafi tsufa da ake da su a cikin dakin karatu na kasar Sin su ne rubuce-rubucen da aka yi a gasussuwan dabbobi da kuma bayan kunkuru a shekaru fiye da 3000 da suka wuce. Dakin karatu na kasar Sin shi kuma dakin karatu ne da aka fi samun lattattafan Sinanci a duk duniya da kuma dakin karatun da aka fi samun littattafan harsunan waje a nan kasar Sin. Ban da wannan, yana tattara wallafe-wallafen da kungiyoyin duniya da gwamnatoci daban daban suka bayar, MDD ta kuma danka masa nauyin ajiye takardunta.

Bisa sauye-sauyen hanyoyin watsa labarai da kuma tasowar hanyoyin sadarwa na zamani, ba ma kawai dakin karatu na kasar Sin ke da kananan abubuwan da ke dauke da bayanai da kayayyakin da ke dauke da bayanai na murya ko hoto, wato AV ba, yana kuma da sansanonin da ke dauke da bayanai, wato database na CD-ROM na gida da kuma waje kusan 100, ga shi kuma da wallafe-wallafe ta hanyar na'urorin zamani.

Dakin karatu na kasar Sin yana kuma da dakin karatu da ake amfani da na'urorin zamani, wato electronic reading library cikin Turanci,wanda ya fi girma a nan kasar Sin, wanda kuma ke da sansanonin da ke dauke da bayanai, wato database, da kuma wallafe-wallafe ta hanyar na'urorin zamani wadanda ke shafar ilmin zaman al'umma da kuma ilmin kimiyya.

An fara aikin neman tafiyar da dakin karatu na kasar Sin ta hanyar zamani a tsakiyar shekarun 1970. A shekara ta 1989, an fara aiki da babban tsarin na'urori masu kwakwalwa na kula da dakunan karatu, don neman bunkasa da yin amfani da fasahohin zamani wajen tafiyar da dakin karatu.Ya zuwa shekara ta 2003 kuma, an fara tafiyar da tsarin nan na ALEPH500 na kula da dakunan karatu daga dukan fannoni.

Yayin da ake kara yin amfani da fasahohin na'urori masu kwakwalwa da kuma fasahohin internet, dakin karatu na kasar Sin ya kuma yi kokarin shigo da fasahohin zamani a cikin ayyukansa daban daban, don neman gaggauta sauya kansa zuwa dakin karatu na zamani. Tun daga shekara ta 1995, dakin karatu na kasar Sin ya fara yin nazari a kan dakin karatu na zamani, wato digital library a bakin Turawa, kuma a shekara ta 2001, a hukunce ne majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta amince da aikin gina digital library na kasar Sin, gwamnatin kasar Sin ta kuma ware kudin da yawansa ya kai kudin Sin yuan biliyan 1 da miliyan 235 ga wannan aiki.

To, masu sauraro, tilas ne mu dasa aya a nan. Tare da fatan malam Ahmad Ilyasu Bawa ya gamsa da bayanin, kuma masu sauraronmu za su ci gaba da rubuto mana wasiku, ni Lubabatu daga nan Beijing ke cewa, ku huta lafiya.(Lubabatu Lei)