Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 15:49:12    
Kasar Sin ta fara tsara dokar haramta mallaka don daukar matakin hana mallaka da neman yin gasa da kyau

cri
A ran 27 ga watan nan da muke ciki, hukumar kafa dokoki na kasar Sin ta fara duba takardar dokar haramta mallaka. A cikin wannan takardar haramta mallaka, an tanada manyan ka'idoji da tsari na haramta mallaka, kuma a fili ne an tsaida cewa, za a kafa kwamitin haramta mallaka da hukumomin haramta mallaka. Yanzu ga wani labarin da wakilin rediyonmu ya rubuto mana filla filla:

Cikin 'yan shekaru da suka shige, sassa daban daban na kasar Sin sun nuna rashin amincewa ga mallakar da akan yi kan sana'o'I iri daban daban, misali a kan sasssan sadarwa da hanyoyin jiragen kasa da karfin lantarki da na kudi. A kan haka ne shugaban ofishin kula da dokokin shari'a na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya bayyana cewa,makasudin kafa dokar haramta mallaka shi ne don yin adawa da hana aikace aikacen mallaka na gida da na kasashen waje da kiyaye halalliyar moriya ta masu saye saye, ya ce, a cikin wannan dokar haramta mallaka, an dauki abubuwa masu kyau daga duk duniya don kara kyautata wannan dokar haramta mallaka ta kasar Sin. Kuma an hana yin ciniki tare da karfi da bin hanyoyin maras kyau. Ya kuma bayyana cewa, tsara dokar haramta mallaka da fara aiwatar da ita wannan zai iya gano da hana aikace aikacen lahanta ci gaban tattalin arzikin kasa.

Koda yake, har yanzu an fara tsara dokar haramta mallaka, amma an ritga an fara aiwatar da "dokar hana yin gasa ba bisa halalliyar dabara ba" cikin dadewa, an riga an tsaida cewa a fili ne an hana mallaka. A kasar Sin yawancin mutane sun sa lura sosai ga matsalar kayade yin gasa ta hanyar siyasa, a cikin wannan dokar haramta mallaka, an kebe wani babi don bayyana hakikanin abubuwa na game da matsalar nan.

Wannan shugaban ofishin kula da tsarin shari'a na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ci gaba da cewa, a cikin wannan dokar haramta mallaka, abubuwan da aka tanada a ciki sun bayyana cewa,gwamnati ta sa muhimmanci sosai ga hana yin gasa ta hanyar siyasa. Wani babban aiki shi ne majalisar gudanarwa ta kasar Sin za ta kafa kwamitin haramta mallaka da hukumomin zartasawa na haramta mallaka, don neman sulhuntawa da zartaswa ga ayyukan haramta mallaka.

A kan matsalar kiyaye ikon mallakar ilmi, an tanada abubuwan game da hana lahanta moriyar masu saye saye kuma za a ci gaba da kyautata tsarin dokokin kiyaye moriyar masu saye saye. Wannan shugaban ofishin kula da tsarin dokokin shari'a na majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya ci gaba da cewa, koda yake yanzu an fara kafa dokar haramta mallaka, amma har yanzu ba a fara tsara dokokin shari'a na tattalin arziki ba tukuna, domin wannan yana danganne da moriyar masu saye saye sosai da sosai.

A cikin wani dakin cinikin sadarwa na birnin Beijing, wakilinmu ya tambayi wata malama da take biyan kudin sadarwa, sai ta nuna kin yardarta ga kudin nan mai tsada haka, bayan da ta ji abubuwan da wakilinmu ya bayyana mata game da kafa dokar haramta mallaka sai ta yi farin ciki cewa, ina fatan wannan dokar haramta mallaka za ta kawo mana babbar moriya wajen biyan kudin shiga motoci da jiaragen kasa da na jiragen sama da na sashen sadarwa.(Dije)