Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 14:44:31    
Kasar Afirka ta Kudu, kasa ce mai girma wajen tattalin arziki

cri

Jamhuriyar kasar Afirka ta Kudu tana kuryar kudancin nahiyar Afirka, kasar ta kudu da gabas da kuma yamma suna fuskatar tekun Indiya da na Atlantic yayin da kasar ta arewa tana makwabtaka da kasashen Namibia da Botswana da Zimbabwe da Mozambique da kuma Swaziland.

Murabba'in yankin kasar Afirka ta Kudu ya kai kusan kilomita miliyan 1.22, kuma yawan mutanen kasar ya kai miliyan 46.6 wadanda suka hade da bakaken fata da fararen fata da masu launin fata da kuma zuriyoyin kasashen Asiya. 'yan kasar Afirka ta Kudu suna yin amfani da Turanci da harshen Afrikaans, haka kuma mazaunan kasar suna bin addinan Christianism da Musulunci da sauransu. Kasar Afirka ta Kudu kasa ce da ita kadai a duniya da ke da manyan birare uku, wato baban birnin siyasa Pretone da babban birnin kafa dokoki Capetown da kuma babban birnin shari'a Bloemfontein.

A shekara ta 1652, 'yan mulkin mallaka na kasar Holand sun shiga kasar Afirka ta Kudu, kuma sun fara habaka girman yankuna daga Cape of Good Hope zuwa arewa. A tsakiyar karni na 19, Turawa masu yawa musamman ma 'yan kasar Birtaniya sun kutsa kai cikin kasar domin neman samun lu'u lu'u da zinariya. Daga shekara ta 1899 zuwa 1902, 'yan kasar Birtaniya da 'yan kasar Holand sun ta da yaki tsakaninsu domin samun kasar Afirka ta Kudu, a karshe dai kasar Birtaniya ta ci nasara. A cikin shekara ta 1910, kasar Birtaniya ta fara hada wasu jihohin kasar Afirka ta Kudu tare domin su kasance cikin kasashen renon Ingila.

A ran 31 ga watan Mayu na shekara ta 1961, kasar Afirka ta Kudu ta janye jiki daga kasashen renon Ingila, kuma ta kafa jamhuriyar kasar Afirka ta Kudu. Yayin da fararen fata na kasar suke kan karagar mulkin kasar, sun gudanar da manufar wariya da nuna bambacin launin fata a cikin kasar. Domin kau da tsarin, jama'ar kasar sun yi gwagwarmaya a karkashin shugabancin kungiyar ANC, a karshe dai sun ci nasara. A watan Afril na shekara ta 1994, karo na farko ne an shirya babban zabe da 'yan kabilu daban daban suka iya shiga a cikin Afirka ta Kudu, kuma ANC ta ci nasara, ta haka Mr. Mandela ya zama shugaba na farko bakar fata a cikin kasar.

Kasar Afirka ta Kudu ta yi suna sosai a duk duniya domin albarkatu iri daban daban, kuma tana daya daga cikin manyan kasashe biyar da suke samar da ma'adinai.

Ban da wannan kuma kasar Afirka ta Kudu kasa ce mafi girma a duk duniya wajen samar da zinarin da kuma sayar da shi zuwa kasashen waje, jimlar zinarin da aka sayar da shi zuwa waje ta kai sulusi na dukkan jimlar kayayyakin da ake sayar da su zuwa waje.

An fara kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Afirka ta Kudu a ran 1 ga watan Janairu na shekara ta 1998. kuma bayan haka, manyan jami'an kasashen biyu su kan kai wa juna ziyarar aiki, kuma ana raya dangantakar hadin kai ta aminci tsakanin kasashen biyu sosai a fannonin siyasa da tattalin arziki da al'adun gargajiya. kasar Afirka ta Kudu abokiya ce ta farko ga kasar Sin wajen cinikayya a cikin dukkan kasashen Afirka. Bisa kidayar da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta bayar, an ce, a cikin shekara ta 2005, jimlar cinikayya tsakanin kasashen Sin da Afirka ta Kudu ta kai dala biliyan 7.27, wato ke nan ta karu da kashi 23 cikin dari idan an kwatanta ita da na makamancin lokaci na shekara ta 2004.(Kande Gao)