Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-28 09:34:18    
Gasar cin kofin duniya ta jarraba karfin da kungiyoyin kasashen Asiya suke da shi wajen buga kwallon kafa

cri

Jama'a, kun san cewa, tun cikin dogon lokaci, kungiyoyi masu karfi na kasashen Turai da na Amurka ta Kudu suna taka muhimmiyar rawa a gun gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa da aka saba yi sau daya a duk shekaru hudu. Amma lallai ba a tafi an bar kungiyoyin kasashen Asiya baya ba a 'yan shekarun baya, wato ke sun samu babban ci gaba wajen wasan. Gasar cin kofin duniya ta shekarar 2006 da ake yi yanzu a kasar Jamus, ta zama tamkar wani ma'auni ne na gwada karfin da kungiyoyin kasashen Asiya suke da shi wajen buga kwallon kafa.

Lallai ba a manta ba, a gun gasar cin kofin duniya da aka yi a kasashen Korea ta Kudu da kuma Japan yau da shekaru 4 da suka gabata, kungiyoyin kasashen Asiya sun ba mutane mamaki domin kungiyar kasar Korea ta Kudu wato mai masaukin baki ta kafa tarihi har ta samu damar shiga cikin jerin kungiyoyi hudu masu karfi. Wannan ya zama sakamako mafi kyau da wata kungiyar Asiya ta samu a gun gasar cin kofin duniya; Kungiyar kasar Japan ma ta sami damar shiga cikin jerin kasashe dake kan matsayin gurabe 16 na farko a duniya a gun gasar.

Ga shi yanzu ana nan ana gudanar da gasar cin kofin duniya ta 18 ta wasan kwallon kafa a Turai. Abun bakin ciki, shi ne dukkan kungiyoyin kasashen Asiya sun sha kaye daga hannun abokan karawarsu, wato ba su samu damar shiga wasanni na zagaye na biyu ba. Amma duk da haka, Jagoran kungiyar wakilan kasar Iran Mr. Sahrukhi Homallon ya bayyana ra'ayinsa, cewa:' A ganina, kungiyoyin kasashen Asiya sun yi rawar gani a gun gasar. Ko da yake dukansu sun sha kaye daga hannun abokan karawarsu, amma sun nuna himma da kwazo wajen buga kwallo. Abun bakin cikin, shi ne ba su yi sa'a ba lokacin da suke saka kwallo a gidan abokan karawarsu.'

Jama'a masu sauraro, kun riga kun samu labarin, cewa a gun gasar cin kofin duniya da ake yi, kungiyoyin kasashen Asiya sun kara da na Afrika har sau uku, wato kungiyar Korea ta Kudu ta lashe ta kasar Togo da ci 2 da 1 ; kungiyar Saudiyya ta yi kunnen doki da ta Tunisia da ci 2 da 2 kuma kungiyar Iran ta yi kunnen doki da ta Angola da ci 1 da 1. A cikin tarihin gasar cin kofin duniya, wannan dai ya zama karo na farko ne da kuniyoyin kasashen Asiya suka samu kyakkyawan sakamako kamar haka lokacin da suke kara da kungiyoyin kasashen Afrika. Abun da ya cancanci a ambata a kai, shi ne kungiyar kasar Korea ta Kudu ta fi nuna gwanita cikin kungiyoyin kasashen Asiya. A cikin wasa na farko, ta lashe ta kasar Togo da ci 2 da 1 ; Daga baya dai, ta yi kunnen doki da kungiyar Faransa da ci 1 da 1, wadda take kunshe da 'yan wasanni taurari da dama har ta taba zama zakara a gasar cin kofin duniya da aka yi a shekarar 1998. Mr. Homallon ya buga babban take ga kungiyar Korea ta Kudu, cewa : 'Lallai kungiyar Korea ta Kudu ta fi yin rawar gani a gun gasar a cikin kungiyoyin kasashen Asiya. Ko shakka babu, kyakkyawar halayyar da ' yan wasan Korea ta kudu suka nuna ta shaida cewa su ne nagartattun wakilai na wasan kwallon kafa na kasashen Asiya'.

Ba kuwa abin mamaki ba ne ganin yadda kungiyar kasar Korea ta Kudu ta nuna rawar gani a gun gasar domin a ' yan shekarun baya sun aika da wassu nagartattun ' yan wasa zuwa kasashen Turai don shiga gasannin da akan yi tsakanin kungiyoyin league-league na sana'a dake bisa matsayin koli wajen buga wasan kwallon kafa ; Ban da wannan kuma, kungiyar Korea ta Kudu ta nace ga gayyatar nagartattun masu koyar da wasan kwallon kafa ' yan asalin ketare don su koyar da 'yan wasan kungiyar. Yin haka, ya kara kyautata dabarun zamani da kungiyar take da su wajen buga kwallon.

Lokacin da muke zantawa kan wasan kallon kafa na Asiya, wajibi ne mu ambaci kungiyar kasar Australiya. Da yake an shigar da wannan kungiya cikin hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya a shekarar 2005, shi ya sa aka dora ta cikin jerin kungiyoyin kasashen Asiya. Game da wannan, Mr. Homallon ya fadi, cewa : ' Shigar da kungiyar Australiya cikin hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta Asiya zai kara daga matsayin karfin da kungiyoyin kasashen Asiya suke da shi wajen buga kwallo ; kuma ya kasance tamkar kalubale ne ga kasashen Korea ta kudu ,da Japan da kuma Iran da dai sauransu wadanda suka gwanance wajen buga kwallo a Asiya'. ( Sani Wang )