A hakika, an sha yin jita-jita game da wanda zai gaji John Snow, ministan kudi na Amurka. Manazarta sun nuna cewa, har kullum dai, shugaba Bush yana son neman wani wanda ke da gwaninta a fannin harkar kudi da tattalin arziki a sa'in da yake iya yada manufofin tattalin arziki don ya karbi mukamin nan na ministan kudi, kuma Henry Hawking shi ne wanda yake nema.
Amma hasali ma dai, Henry Hawking ba sabon hannu ba ne a fagen siyasa na Washington. Tuni a shekarar 1970 har zuwa ta 1972, Mr.Hawking ya taba samun aiki a Pentagon, har ma ya taba zama mai taimakawa mataimakin ministan tsaro. Kafin ya shiga kamfanin Goldman Sachs kuma, ya taba zama mataimaki na shugaba Nickson a fadar White House ta Amurka. Game da gabatar da sunan Henry Hawking a matsayin wanda ake son ba shi mukamin ministan kudi, bangarori daban daban na Amurka sun nuna ra'ayi mai yakini. A cewar majalisar dattawa kuma, za a zartas da wannan gabatarwa tun da wuri.
Kamfanin Goldman Sachs wanda ke da tsawon tarihi na shekaru sama da 130, ya taba kasancewa daya daga cikin muhimman bankunan zuba jari na Wallstreet. Hedkwatar kamfanin nan yana birnin New York, bayan haka kuma, yana da hedkwatoci na shiyya shiyya a biranen London da Tokyo da kuma Hongkong, ofisoshinsa kuma sun barbazu ko ina a shiyyoyin Amurka da Turai da Asiya da kuma tekun Pasifik. A shekara ta 1994, kamfanin Goldman Sachs ya sami shigowa cikin kasuwar babban yankin kasar Sin, kuma ya kafa ofishinsa a birnin Shanghai da na Beijing.
Ana iya cewa Mr.Hawking yana daya daga cikin manyan mutanen Wallstreet wanda ya fi kulla abuta da kasar Sin. A cikin shekaru 15 da suka gabata, Henry Hawking shi da kansa ne ya kawo wa kasar Sin ziyara har sau fiye da 70. A karkashin jagorancinsa, kamfanin Goldman Sachs ya zo na farko a fannoni da dama a tsakanin hukumomi masu jarin waje a kasar Sin. Bayan haka, shi kuma shugaba ne wanda ya kafa kwamitin ba da shawara na kwalejin koyon ilmin gudanar da tattalin arziki na jami'ar Tsinghua ta kasar Sin, yana kuma kan kujerar mai ba da shawara a jami'ar. Ban da wannan, a watan Yuni na shekara ta 2003, wato lokacin da aka fi fama da cutar Sars, Mr.Hawking ya kawo ziyara a birnin Beijing duk da tsananin cutar, wannan kuma ya burge mutane sosai.
Manazarta sun nuna cewa, babbar matsala da sabon ministan kudin Amurka zai fuskanta bayan da ya kama mukaminsa shi ne yaya zai daidaita manufar Amurka a kan kasar Sin, kuma daidaita batun darajar musanyar kudin Sin yana daya daga cikin kalubalen da Mr.Hawking zai fuskanta. Amma manazarta sun kuma yi imanin cewa, zumuncin da Mr.Hawking ke da shi ga kasar Sin zai taimaka wajen daidaita huldar tattalin arziki da ciniki da ke tsakanin Sin da Amurka.
|