Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-27 15:47:21    
Abincin lardin Sichuan na kasar Sin

cri

Lokacin da muka tabo magana a kan lardin Sichuan da ke yammacin kasar Sin, ban da wasu shahararrun tsaunuka da babban buddah, abin da ya fi burge masu yawon bude ido shi ne abincin Sichuan wanda ke da dandano na musamman. Abincin Sichuan yana daya daga cikin manyan rukunonin abinci 8 na kasar Sin, kuma yana da tarihi har na tsawon shekaru sama da 2000.

Hali na musamman na abincin Sichuan shi ne yaji. Sabo da kasancewar lardin Sichuan a kwari, ga shi kuma akwai damshi a wurin. Sabo da haka, mutanen wurin su kan ci tugande don kawar da damshi. Shi ya sa mutanen wurin suka sami wannan al'ada ta son cin tugande.

Mr. Liu Huaichun, wani kuku a cikin wani babban hotel, ya bayyana cewa, 'Abincin Sichuan yana da yaji da kamshi da kuma dadi. Ma iya cewa, abincin Sichuan ya zo na farko a cikin manyan rukunonin abinci takwas na kasar Sin. Yawancin abincin Sichuan sun sami karbuwa a tsakanin mutane. kamar su abincin nan da ake kira Gongbao Jiding da Mapo Doufu da dai sauransu, duk wadannnan sun shahara sosai.'

Ya zuwa yanzu dai, abincin Sichuan ya riga ya bunkasa har ma yawan ire-irensa ya zarce dubu 4. Idan abincin Sichuan iri iri sun cika tebur, to, ba dama ka sami biyu da suka yi daidai da juna.

Idan kun sami damar zuwa birnin Chengdu, babban birnin lardin Sichuan na kasar Sin, to, sai ka je wasu shahararrun gidajen abinci na wurin, kamar su Caigengxiang da Baidicheng da dai sauransu, ka dandana abincin Sichuan na ainihi. Hasali ma dai, a kasar Sin, ana iya samun abincin Sichuan a ko ina. Misali a birnin Beijing, akwai gidajen abincin Sichuan a ko ina. Mutanen Sichuan sun kuma kara kyautata abincinsu don neman dacewa da al'adun abinci na wurare daban daban. Kukun nan na abincin Sichuan, Mr.Liu ya kara da cewa,'yanzu a birane daban daban, abincin Sichuan ya sami karbuwa sosai, har ma ya zarce sauran rukunonin abinci iri iri. Hanyoyin iri iri da gidajen abinci daban daban suke bi ya bayyana al'adun da ke cikin abincin Sichuan, kuma sun saka al'adun Sichuan a cikin abincin Sichuan. Abincin Sichuan yana iya mallakar kasuwannin wurare daban daban, kuma yana iya dacewa da dandano na mutanen wurare daban daban.'

Kamar dai yadda Mr.Liu ya ce, abincin Sichuan ya sami karbuwa sosai a birane daban daban na kasar Sin. Ko da yake abincin Sichuan na da yaji sosai, amma wasu mutane suna son wannan dandano, har ma wasu suna mutuwar son abincin, idan ba su ci ba, to, kamar ba za su ji dadin zama ba. Zhou Yihu, wani mai sha'awar abincin Sichuan, ya ce, 'wani karo, na ci tattasai hade da naman kaji. Kash, tattasai jajaye sun shimfidu a kan naman kaza, wannan ya burge ni kwarai. Bayan da na dandana kuma, na ji dadi sosai, har ma nan da nan na fara son abincin Sichuan.'

Watakila yanzu kana damuwa da cin abincin Sichuan sabo da tsoron yaji. Amma sai ka kwantar da hankalinka, sabo da ba wai dukan abincin Sichuan ne ke da yaji ba, akwai wasun da ba su da yaji ko kadan. Nan gaba, idan ka sami damar zuwa nan kasar Sin, kada dai ka manta da dandana abincin Sichuan.(Lubabatu Lei)