Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-26 19:51:06    
Kasar Sin ta daidaita tsanancewar maganar miyagun kwayoyi bisa wani matsayi

cri

Tun daga watan Afril na shekarar 2005 da ta gabata, gwamnatin kasar Sin ta tafiyar da harkokin yaki da kwayoyi masu gusar da hankali a duk fadin kasar?wadanda dukan al'ummar kasar suke sa hannu a ciki, wurare daban daban da hukumomin da abin ya shafa sun kara karfin yaki da kwayoyi masu gusar da hankali ta hanyoyin yin rigakafi da hana shan miyagun kwayoyi da yin watsi da al'adar shan miyagun kwayoyi da kuma toshe mafarinsu. A cikin shekarar da ta gabata, kasar Sin ta daidaita tsanancewar maganar miyagun kwayoyi bisa wani matsayi.

Kafin yau ran 26 ga wata, wato ranar yaki da kwayoyi masu gusar da hankali ta duniya, kwamitin yaki da miyagun kwayoyi na kasar Sin ya shirya taron manema labaru a nan Beijing, inda ya bayar da rahoto kan cin gaban aikin yaki da miyagun kwayoyi da kasar Sin take yi tun daga shekarar jiya. Mataimakin babban sakataren kwamitin Mr. Chen Cunyi ya bayyana cewa, a cikin shekarar da ta wuce, hukumomin da abin ya shafa sun tafiyar da harkokin musamman na yaki da miyagun kwayoyi, sun sami sakamako a bayyane.

'mun tafiyar da harkokin musamman a jere, kamar su murkushe fataucin miyagun kwayoyi tsakanin kasa da kasa da kuma shiyya-shiyya da kai bugu ga samar da fataucin sabbin miyagun kwayoyii da kuma yaki da miyagun kwayoyi da halaltar da kazamin kudi, mun dakushe fankamar masu aikata laifuffukan miyagun kwayoyi. A shekarar 2005, mun tona laifuffukan miyagun kwayoyi dubu 45 a duk kasar, mun kama wadanda da ake tuhumarsu da laifuffukan miyagun kwayoyi dubu 58, mun kwace miyagun kwayoyi iri daban daban ton 17.5.'

Yanzu shan miyagun kwayoyi yana barbazuwa a ko ina duniya, kasashe da shiyya-shiyya suna kara fama da miyagun kwayoyi, mafarin miyagun kwayoyi da ire-irensu da yawansu da kuma yawan mutanen da suke shan miyagun kwayoyi suna ta karuwa. Saboda haka, kasar Sin tana fuskantar hali mai tsanani wajen yaki da miyagun kwayoyi.

Domin irin wannan hali ne, a lokacin da take kara karfinta na daidaita wannan batu, a sa'i daya kuma, kasar Sin ta ingiza yin hadin gwiwa da kasashen duniya a fannin yakin da myagun kwayoyi cikin himma da kwazo. Mr. Chen ya ba da karin haske cewa,

'kungiyar ASEAN da kasarmu mun shirya taron duniya na karo na yin hadin gwiwar yaki da miyagun kwayoyi, mun kara yin hadin kai da kasashe masu makwabtaka da mu kamarsu Myanmar da Laos a fannonin yaki da miyagun kwayoyi da ayyukan neman samun bunkasuwa ta sauran hanyoyi a maimakon cinikin miyagun kwayoyi, mun tona laifuffukan fataucin miyagun kwayoyi tsakanin kasashe da shiyyoyi, mun kuma kama manyan 'yan kasuwar fataucin miyagun kwayoyi 20 na kasashen waje, mun ba da gudummowarmu wajen sha'anin yaki da miyagun kwayoyi na duniya.'

A halin yanzu dai, kasar Sin ta kara yin hadin gwiwa da kasashen waje a fannin yaki da miyagun kwayoyi, kasashe da yawa da kasar Sin sun yi hadin gwiwar kama masu fataucin miyagun kwayoyi da kwace miyagun kwayoyi.

Mr. Chen ya yi bayanin cewa, nan gaba, kasar Sin za ta ci gaba da ingiza yaki da miyagun kwayoyi.

'za mu mayar da daidaita maganar Heroin a matsayin muhimmin aiki, za mu ci gaba da kara karfi na aiwatar da dokoki da kama masu fataucin miyagun kwayoyi da kwace miyagun kwayoyi, da toshe mafarin miyagun kwayoyi, da warkar da masu fama da kwayoyi masu gusar da hankali, musamman ma masu fama da Heroin, da sarrafa kwayoyi masu gusar da hankali, da yin furofagandar yaki da miyagun kwayoyi, da kuma kawar da mafarin miyagun kwayoyi a kasashen waje da aikin neman samun bunkasuwa ta sauran hanyoyi a maimakon cinikin miyagun kwayoyi, ta yadda za mu tafiyar da ayyukan yaki da kwayoyi masu gusar da hankali daga dukan fannoni. '

Al'ummar kasar Sin sun sa hannu cikin ayyukan yaki da miyagun kwayoyi da hannu biyu biyu, sun taka muhimmiyar rawa.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, don biyan bukatun ayyukan yaki da kwayoyi masu gusar da hankali, da kuma yin rigakafi da yanke hukunci ga laifuffukan miyagun kwayoyi, kasar Sin tana tsara 'dokar yaki da miyagun kwayoyi. An riga an mika ta ga majalisar gudanarwa ta kasar Sin domin duddubawa, ana sa ran cewa, za a gabatar da ita kafin karshen wannan shekara.(Tasallah)