Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-25 22:10:06    
Firaministan kasar Sin ya kawo karshen ziyararsa a kasashen Afirka 7

cri

A yau ran 25 ga wata, firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya dawo nan birnin Beijing, bayan da ya kammala ziyarar aiki a kasashen Masar da Ghana da Congo Brazzaville da Angola da Afirka ta kudu da Tanzania da kuma Uganda.

A lokacin ziyarar, cikin sahihanci ne Mr.Wen Jiabao ya yi musanyar ra'ayoyi tare da shugabannin kasashe daban daban dangane da inganta huldar da ke tsakanin bangarori biyu da kuma bunkasa sabuwar huldar abokantaka a tsakanin Sin da Afirka, inda kuma suka cimma daidaito a jere. Gaba daya ne Sin da kasashen nan 7 na Afirka suka daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa har 71, wadanda suke shafar fannonin siyasa da tattalin arziki da ciniki da raya manyan ayyuka da al'adu da ilmi da kuma kimiyya da fasaha da dai sauransu.

Bayan ziyarar, ministan harkokin waje na kasar Sin, Li Zhaoxing ya ce, an cimma burin 'karfafa zumunci da kara amincewa da juna da habaka hadin gwiwa da kuma samun bunkasuwa tare' sakamakon wannan ziyarar da firaminista Wen Jiabao ya kai a kasashen Afirka 7, kuma ziyarar za ta kawo babban tasiri a kan bunkasuwar huldar da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka a sabon zamani.(Lubabatu Lei)