Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-25 17:57:10    
Kafofin watsa labaru na kasar Uganda suna mai da hankali sosai a kan ziyarar aiki da Wen Jiabao ya kai wa kasar

cri

A ran 24 ga wata, babbar jarida ta farko ta kasar Uganda wato jaridar 'New Vision' ta bayar da wani sharhi cewa, ziyarar aiki cikin kwanaki biyu da firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao ya kai wa kasar Uganda ta bayyana cewa, kasar Sin tana mai da hankali sosai a kan dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Sharhin ya ce, kasar Sin aminiyar gargajiya ce ta kasashen Afirka, a yayin da kasashen Afirka da yawa suke neman 'yancin kai, kasar Sin ta taba bayar da taimakonta ba tare da son kai ba. Game da kasar Uganda, kasar Sin tana nuna goyon bayanta a fanonnin tattalin arziki da fasahohi da manyan gine gine da dai sauransu. Filin wasanni mai suna 'Mandela' ya zama wani misali mai kyau da kasar Sin ta ba da taimako ga kasar Uganda.

Wannan sharhi ya ci gaba da cewa, kasar Uganda da sauran kasashen Afirka sun sami moriya daga kasar Sin a sauran fannoni da yawa. Tabbas ne saurin bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin zai samar wa Afirka bunkasuwa, kuma za su sami nasarori tare wajen taimakawa juna.(Danladi)