Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-24 20:55:08    
Wen Jiabao ya kammala ziyararsa a kasashe 7 na Afirka

cri
Ran 24 ga wata, firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao ya kammala ziyarar da ya kai wa kasashe 7 na Afirka, ya tashi daga birnin Kampala, hedkwatar kasar Uganda, ya koma gida.

A lokacin ziyararsa a kasar Uganda, shugaban kasar Mr. Yoweri Kaguta Museveni da firaministan kasar Apolo Nsibambi sun yi shawarwai da ganawa da Mr. Wen a ran 23 da ran 24 ga wata.

A gun shawarwarin da ganawar, Mr. Wen ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin tana dora muhimmanci kan raya huldar da ke tsakaninsa da kasar Uganda, zai ci gaba da daukan matakai don kara ingiza yin hadin gwiwa da kasar Uganda a fannoni daban daban. kasar Sin tana son ci gaba da taimakawa kasar Uganda wajen raya ayyukan ba da ilmi da kiwon lafiya da ke kunshe da shawo kan zazzabin cizon sauro da ciwon cutar AIDS.

Mr. Museveni da Mr. Nsibambi sun bayyana cewa, kyautata yin hadin gwiwa da kasar Sin manufa ce da gwamnatin kasar Uganda ke bi. Kasar Uganda tana tsayawa tsayin daka kan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, tana goyon bayan babban aikin dinkuwar kasar Sin gu daya.

A lokacin da Mr. Wen ke ziyarar kasar Uganda, bangarorin 2 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar tattalin arziki da fasaha ta gwamnatocin 2 da takardun yin hadin gwiwa a jere. Sun kuma ba da hadadiyyar sanarwa.(Tasallah)