Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-24 20:33:59    
Firaministan kasar Uganda ya gana da takwaransa na kasar Sin

cri
Ran 24 ga wata, a birnin Kampala, firaministan kasar Uganda Mr. Apolo Nsibambi ya gana da takwaransa na kasar Sin Mr. Wen Jiabao, wanda ke ziyarar kasarsa.

Mr. Nsibambi ya bayyana cewa, kasashen Uganda da Sin suna da hulda mai kyau a tsakaninsu, kyautata yin hadin gwiwa da kasar Sin manufa ce da gwamnatin kasar Uganda ke bi, kuma ba za ta canja ta ba. A tsanake ne kasar Uganda za ta aiwatar da ra'ayi daya a fannoni daban daban da kasashen 2 suka samu, ta yadda za kara samun sakamako wajen yin hadin gwiwa. Ya kuma nanata cewa, kasar Uganda tana tsayawa tsayin daka kan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya, tana goyon bayan babban aikin dinkuwar kasar Sin gu daya.

Mr. Wen ya darajanta gwamnatin kasar Uganda saboda tana tsayawa tsayin daka kan bin manufar kasar Sin daya tak a duniya. Ya kuma bayyana cewa, a lokacin ziyararsa a kasar Uganda, shugaba Museveni da shi sun zurfafa yin tattaunawa kan kara raya huldar da ke tsakanin kasashen 2, sun sami ra'ayi daya a fannoni daban daban. Kasashen 2 sun rattaba hannu kan yarjejeniyoyin yin haidn gwiwa a jere. Ziyararsa ta tabbatar da makasudi na kara wa juna fahimta da amince da kuma ingiza yin mu'amala da hadin gwiwa.(Tasallah)