Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-24 17:42:02    
Kafofin yada labaru na Afirka sun mai da hankulansu kan ziyarar Wen Jiabao a kasashe 7 na Afirka

cri
Firaministan kasar Sin Mr. Wen Jiabao yana kai wa kasashen Masa da Ghana da Congo(Brazzaville) da Angola da Afirka ta Kudu da Tanzania da kuma Uganda ziyarar aiki tun daga ran 17 ga wata. Ziyarar da Mr. Wen yake yi ta jawo hankulan kafofin yada labaru na Afirka sosai.

A kwanan baya, manyan kafofin yada labaru na kasar Angola sun watsa labaru cikin himma da kwazo game da ziyarar da firaministan kasar Sin ya kai wa kasar Angola a karo na farko, sun dora muhimmanci kan sakamakon da aka samu daga ziyarar Mr. Wen da kuma yarjejeniyar yin hadin gwiwa da bangarorin Angola da Sin suka rattaba hannu a kai.

Babban edita mai kula da aikin buga jaridar Guardian, wadda ita ce mafi girma a kasar Tanzania, ya bayyana cewa, ba ma goyon baya a fuskar kayayyaki kawai ba, har ma kasar Tanzania ta sami goyon baya daga kasar Sin a fuskar ra'ayi. Kasar Tanzania tana koyon yadda za a raya tattalin arziki daga nasarorin da kasar Sin ta samu daga wajen yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga kasashen waje.

Wasu muhimman jaridu na kasashen Uganda da Zambia da Zimbabwe su ma sun zura idanunsu kan ziyarar da firaminista kasar Sin ke kai wa Afirka.(Tasallah)