Ran 23 ga wata, a birnin Kampala, firaministan kasar Sin Wen Jiabao, wanda ke ziyarar kasashen Afirka, ya yi shawarwari da shugaban kasar Uganda Mr. Yoweri Kaguta Museveni.
A gun shawarwarin, Mr. Wen ya bayyana cewa, bangaren kasar Sin tana dora muhimmanci kan raya huldar da ke tsakaninta da kasar Uganda, ya riga, zai kuma ci gaba da daukan matakai a jere don kara sayen abubuwa daga kasar Uganda. Bangaren kasar Sin yana sa kaimi kan masana'antunsa da su zuba jari a kasar Uganda, su sa hannu cikin ayyukan noma da yin amfani da ruwa da sufuri da aikin sadarwa da manyan ayyuka. Kasar Sin tana son ci gaba da taimaakwa kasar Uganda wajen raya sha'anonin ilmi da kiwon lafiya, wadanda ke kunshe da shawo kan zazzabin cizon sauro da ciwon cutar AIDS.
A nasa bangaren kuma, Mr. Museveni ya ce, kasar Uganda ta ci riba daga wajen bunkasuwar kasar Sin, kasar Uganda tana fatan kara yin hadin gwiwa da kasar Sin wajen ayyukan noma da sufuri da sadarwa da samar da ma'adinai da yawon shakatawa da manyan ayyuka. Bunkasuwar kasar Sin wata dama ce, ba barazana ba ce, wadda take amfanawa kasar Uganda da Afirka da kuma duk duniya a fannonin zaman lafiya da bunkasuwa.(Tasallah)
|