Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2006-06-24 17:16:40    
Kasashe 16 sun shiga mataki na biyu na wasannin cin kofin duniya

cri

Ran 23 ga wata, bayan kasashen Ukraine, Faransa da Switzerland sun shiga jerin kasashe 16 mafiya nagarta, an tabbatar da duk kasashe 16 wadanda suka shiga mataki na biyu na wasannin cin kofin duniya na shekarar 2006 a kasar Jamus.

A cikin gasannin da aka yi a tsakanin kungiyoyin rukuni H, kungiyar Spain ta ci kungiyar Saudi arabia da 1 da ba nema, yayin da kungiyar Ukraine ta ci ta Tunisia da 1 da ba nema.

A cikin gasanin rukuni G, kasar Switzerland ta ci ta Korea ta kudu da 2 da ba nema, kuma kungiyar Faransa ta ci ta Togo da maki iri daya. Kungiyoyin Switzarland da Faransa sun shiga jerin kasashe 16 mafiya nagarta tare.

Gasannin da za a yi a cikin mataki na byu su ne: Yau Jamus za ta yi kara da Sweden, sa'annan daga baya Argentina ta yi wada da Mexico. Ecuador za ta yi wasa da England, sa'annan Portugal ta yi wasa da Holland, Italiya za ta kara Austrilia, Ghana wadda an nada sunanta "Brazil ta Afirka" za ta kara Brazil, Switzerland za ta yi wasa da Ukraine, kuma Faransa za ta yi wasa da Spain.